Tsohon shugaban hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribadu ya musanta batun cewa ya karbi kudi a hannun Sambo Dasuki.
A wani jawabi da ya fitar a jiya, Malam Ribadu ya bayyana cewa wadanda suke kokarin bata masa suna a kafafen yada labarai su fito da hujjojin su na cewa ya karbi kudi a wurin Dasuki.
“Na samu labarin cewa wai na dawo da wasu kudade da na karba a wurin Dasuki", inji Malam Nuhu.
Ya kuma kara da cewa "Bari na sanar da ku cewa ba ni da wata alaka da Dasuki a lokacin da yake kan mukami. Ba zan iya tuna rana ta karshe da na hadu da shi ba tun bayan da aka ba shi wannan matsayi.
"Don haka ya zama dole na yi mamaki idan aka ce na karbi kudi a wurin wanda ba ni da wata alaka da shi balle ma a ce mayar da kudin da ya ba ni".
Idan za a iya tunawa dai, yanzu haka ana kan bincikar Sambo Dasuki kan dala bilyan 2.1 na kudin sayen makamai.
Title :
Ban Karbi Ko Sisin Kobo A Wurin Dasuki Ba, Inji Nuhu Ribadu
Description : Tsohon shugaban hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribadu ya musanta batun cewa ya karbi kudi a hannun Sambo Dasuki. A wani jawabi da ya fitar a jiy...
Rating :
5