, Bayan An Yanke Musu Hukuncin Kisa Sakamakon Yin Bore
Sojojin da aka yi wa afuwa a watan Agustar bara, bayan a farko an yanke musu hukuncin aikata laifin bijire wa umurnin shugabanninsu a yaki da Boko Haram, sun ki amincewa da sake tura su bakin daga a yankin Arewa maso gabashin kasar nan da aka yi.
Sojojin dai na zargi hukumomin su ne da wulakanta su a tsawon lokacin da aka ce an yi musu afuwa, a saboda haka ne ma suke gani, afuwar da aka ce an musu, ba da gaske ba, sannan suka yi zargin an sake tura su bakin daga ne don a halaka su.
Sojojin wadanda suka haura dubu uku, suna daga cikin kimanin dubu biyar da aka samu da aikata laifuka daban daban.
A cewar sojojin, su a wurinsu, ba a mayar da su aikin soja ba, tunda har yanzu babu wani bangare da rundunar sojin kasar da ya karbe su.
Kazalika sun ce babu wani horo na hakika da aka ba su, inda suka yi zargin cewa shugabanninsu, sun ta tara su ne kawa suna wulakanta su ta ce musu matsorata.
Sai dai rundunar sojin Najeriyar ta nuna rashin jin dadi da halayyar wasu sojojin, inda ta ce babu gaskiya a zarge zargen da sojojin keyi.
Rundunar sojin a cikin wata sanarwa da kakakinta Kanar Sani Usman Kukasheka ta ce ba za ta amince da rashin da'a ba, sannan ta ce duk wanda ba zai iya bin dokokin aikin soja ba, to kofa a bude ta ke ya yi waje.
Title :
Ba Za Mu Koma Fagen Daga Da Boko Haram Ba, Inji Sojojin Da Aka Yi Wa Afuwa
Description : , Bayan An Yanke Musu Hukuncin Kisa Sakamakon Yin Bore Sojojin da aka yi wa afuwa a watan Agustar bara, bayan a farko an yanke musu hukunci...
Rating :
5