Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan sanannen malamin mabiya mazhabar Shi'a, Nimr al-Nimr, a kasar.
Ministan cikin gida na kasar ya ce malamin yana cikin jerin mutane 47 da aka yanke wa hukuncin kisa bayan da aka same su da laifukan ta'addanci da suka jibanci sukar masarauta.
A shekarar 2012 ne dai a ka tsare Nimr bayan da ya kalubalanci tsarin sarautar kasar ta Saudiyya.
Wani dan uwan malamin ya ce iyalan Nimr sun girgiza da labarin zartar da hukuncin.
Tuni dai shugabannin Iran suka yi tir da zartar da hukuncin.
Title :
An Zatar Da Hukuncin Kisa Wa Malamai Shi'a A Saudi
Description : Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan sanannen malamin mabiya mazhabar Shi'a, Nimr al-Nimr, a kasar. Ministan cikin gida na kasar ya ...
Rating :
5