Wani jagoran kungiyar Boko Haram mai suna Jarasu Shira a safiyar yau Laraba ya shiga hannu a garin Damboa dake jihar Borno, kamar yadda majiyarmu ta Daily Trust ta rawaito.
An kama shine a tashar mota da misalin karfe 8:30 na safe tare da wasu mutane goma da suka yi masa rakiya, wadanda ake zargin su ma 'yan kungiyar ne, inda yake shirin barin garin Damboa zuwa jihar Lagos. Membobin 'yan banga ne suka yi nasarar cafke shi.
Wata majiya ta bayyana cewa Shira, wanda ake yi wa lakabi da Jarido, shine na daya a hotunan 'yan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo.
Title :
An Kama Jagoran Boko Haram Da Wasu Membobinta Guda Goma
Description : Wani jagoran kungiyar Boko Haram mai suna Jarasu Shira a safiyar yau Laraba ya shiga hannu a garin Damboa dake jihar Borno, kamar yadda maj...
Rating :
5