A cikin karshen makon da ya gabata ne wata Bafulatana mai suna Adama Sani ta haifi jarirai guda biyu manne da juna.
Adama ta haifi jariran ne a wata Ruga da ake kira Tongo, dake cikin karamar hukumar Ganjuwa a jihar Bauchi, inda daga bisani aka garzaya da ita asibitin koyarwa na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU).
Kasancewar mai jegon da 'yan uwanta marasa karfi ne, yanzu haka ana neman taimako domin raba yaran.
Title :
An Haifi Tagwaye Manne Da Juna A Jihar Bauchi
Description : A cikin karshen makon da ya gabata ne wata Bafulatana mai suna Adama Sani ta haifi jarirai guda biyu manne da juna. Adama ta haifi jariran...
Rating :
5