Limamin cocin Adoration Ministries dake jahar Enugu, pastor Ejike Mbaka ya bayyana cewa akwai wasu mutane dake yunkurin ganin bayan shugaban kasar Najeria, Janar Muhammadu Buhari.
Paston ya bayyana hakan ne yayin da yake gudanar da addu’o’in murnar shiga sabuwar shekara tare da mabiyansa a safiyar ranar Juma’a.
Inda ya bayyana cewa akwai wasu mutane daga cikin wadanda sukayi sama da fadi da kudaden al’umma a gwamnatin baya ta tsohon shugaban kasa wato Goodluck Jonathan dake kokarin kitsa wannan mugun abun.
Suna so su kashe Buhari ne saboda su sami damar cigaba da handama da facaka da kudaden talakawa kamar yadda suka saba a gwamnatin baya data gabata domin sun tabbatar da cewa Buhari bazai basu damar aiwatar da hakan ba a gwamnatinsa.
Sannan Mbaka ya shawarci shugaba Buhari da ya kula da kansa sannan ya kuma cigaba da aikin alherin da ya dauko na yaki da cin hanci da rashawa ba tare da yaji tsoron wata barazana daga wani ba.
Source Arewamobile
Title :
AKwai Masu Yunkurin Kashe Buhari – Rev Mbaka
Description : Limamin cocin Adoration Ministries dake jahar Enugu, pastor Ejike Mbaka ya bayyana cewa akwai wasu mutane dake yunkurin ganin bayan shugaban...
Rating :
5