Idan ka duba cikin manyan litattafan Tarihin Musulunci, wanda manyan Malaman Musulunci suka wallafa, irin su Zahabiy, Ibnu Katheer, Halbiy, Ibnu Sa'adin Ibnu Jareer da sauransu, zaka tarar sun ware babi na musamman wanda sukan yi bayani akan abubuwan mamakin da suka bayyana alokacin haihuwar Manzon Allah (saww).
Wasu abubuwan sun faru ne daf da lokacin haihuwarsa. Wasu kuma sai bayan an haifeshi.
Akwai hadisi wanda Baihaqiy da Ibnu Asakira suka ruwaito tare da isnadi zuwa ga Hani'ul Makhzoumiy (ra) yace:
"Yayin da daren haihuwar Manzon Allah (saww) yayi, sai Zankon nan na fadar Kisra (sarkin daular Farisa) ya girgiza (ya ja junansa).
Ginshikai guda goma sha hudu suka zubo daga ciki. Kuma wutar nan ta Farisa (wacce suke bauta mata) ita ma ta mutu.
Kafin haihuwar Manzon Allah (saww) kuwa, wutar ta fi shekaru dubu bata mutu ba. Kogin nan na garin Saawata shima ya Qafe (shima suna bauta masa ne).
(aduba DALA'ILUN NUBUWWAH NA BAIHAQIY juzu'i na 1 shafi na 126-129 hadisin yana nan da tsawonsa).
Ibnu Jareer At-Tabariy ma ya kawoshi acikin Kitabut Tarikh juzu'i na 2 shafi na 131-132.
Hafizul 'Iraaqiy ya ruwaitoshi shima acikin littafinsa AL-MAURID shafi 11.
Malamai Muhakkikai suka ce Zubowar ginshikai sha-hudu din nan yana ishara ne zuwa ga cewar babu abinda ya saura daga wannan daular kafircin sai mulkin sarakuna goma sha hudu.
Kuma hakan ne ya faru. Allah ya kawo Qarshen mulkinsu a zamanin Khulafa'ur Rashidun.
Ita kuma wannan wutar ta mutanen farisa, sun kasance sama da shekary dubu suna bauta mata. Ko yaushe dare da rana akwai masu hurata. Basu bari ta mutu. Amma lokacin da aka haifi Manzonmu (saww) sai suka wayi gari suka ganta ta mutu agabansu suna kallo.
Shima wannan yana isharah ne zuwa ga cewar lallai an haifi Annabin da zai bushe wutar kafirci (saww).
Shi kuwa Qafewar wannan babban kogi na garin Saawata, wanda har jiragen ruwa sukan bi ta cikinsa, amma aka wayi gari ya Qafe, isharah ce da take nuna cewar an haifi Annabin da zai dakatar da yaduwar kafirci aduniya.
Daga cikin manyan ayoyin da suka bayyana alokacin haihuwarsa (saww) akwai Jifar shaitanu da aka rika yi.
Wato kafin zuwan Manzon Allah (saww) shaitanun Aljanu sun kasance suna hawa kan junansu, wannan akan wannan har sai sun kusanci jikin Sama-ta-daya.
Anan zasu rika sauraron maganar da Mala'iku suke yi atsakaninsu dangane da abubuwan da zasu faru aduniya. To da zarar sunji, sai su kuma su rika gaya ma junansu, har dai su gaya ma Bokaye da masu bautar gumaka. Don haka bokaye suna da tasiri awancan lokacin.
Amma tun daga ranar da aka haifeshi (saww) sai Allah ya sanya Mala'ikunsa suka tsare sararin Samaniya. Babu damar wani Shaitani ya wuce ta wajen sai sun jefeshi da garwashin Wuta.
Hakanan bayan an fara yi masa wahayi ma abin ya kasance. Kuma haka abinyake har yau.
Ibnu Katheer ma ya ruwaito cewar alokacin da aka haifi Manzon Allah (saww) sai da Iblees (L. A) yayi Eehu yayi kururuwa. Irin wacce yayi alokacin da Allah ya la'anceshi, da kuma lokacin da aka koreshi daga cikin Aljannah, da kuma lokacin da aka saukar da surar nan ta fatiha.
Alhafizul 'Iraqiy duk ya kawo wadannan bayana acikin MAURIDUL HANA.
Kuma yana daga cikin wannan, cewa duk gumakan duniya sun wayi gari an kifesu akan fuskokinsu. Kamar yadda Ibnu Abid Dunya ya ruwaito tare da Isnadai Sahihai acikin KITABUL HAWATIF yace an rika jin maganganu da muryoyi suna fitowa daga bakin Gumaka aranar da aka haifi Manzon Allah (saww) da kuma ranar da aka aikoshi (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam).
Anan zamu tsaya sai a karatu ba gaba in sha Allahu zamu dora daga nan. Da fatan Allah shi Qara mana son Manzon Allah (saww) da iyalan gidansa, ya Qara mana riko da koyarwarsa (saww).
An gabatar da wannan karatun ne a Zauren Fiqhu Whatsapp (1) aranar Juma'a 21 ga Rabee'ul Awwal 1437. Daidai da 1-1-2016.
Duk wanda yake Qaunar Allah da Manzonsa (saww) ya dena kwafar rubutunmu yana chanza masa launi.. DON GIRMAN ALLAH!!
Title :
Abubuwan Mamaki Da Suka Bayyana A Lokacin Haihuwarsa [SAWW]
Description : Idan ka duba cikin manyan litattafan Tarihin Musulunci, wanda manyan Malaman Musulunci suka wallafa, irin su Zahabiy, Ibnu Katheer, Halbiy, ...
Rating :
5