*Kimanin Matanmu 300 Ne Suke Tsare A Hannun Hukuma
Shugaban rundunar sojojin Nijeriya, Liyutanal Janar Tukur Buratai ya bayyana a jiya Alhamis cewa Jagoran mabiya Shi’a, Sheik Ibrahim Zakzaky ba ya komar sojoji.
Buratai ya bayyana hakan ne a yayin da kungiyar harkokin addinin Musulunci ta kololuwa (NSCIA) ta kawo masa ziyara hedikwatar rundunar tsaron da ke Abuja.
Shugaban sojojin, wanda ya mayar da martani a yayin da kungiyar ta NSCIA ta bukaci ta gana da Sheik Zakzaky, Buratai ya bada amsar cewa sun mika Malamin sashen da ya kamata a bincike shi.
Sannan kuma ya kara da cewa hukuma ba za talamunta da duk wata dabi’a da ta saba doka ba, musamman a daidai lokacin da wani sashe na kasar ke fama da ‘yan ta’adda.
A gefe daya kuma, mai magana da yawun ‘yan Shi’an, Ibrahim Musa ya bayyana cewa kimanin mata dari uku ne daga cikin membobinsu ke tsare a hannun rundunar tsaron, inda ya kara da cewa wasu daga cikin su suna tsare ne ba tare da an yi musu jinyar raunin da suka samu ba.
Title :
El Zakzaky Ba Ya Hannunmu, Inji Buratai
Description : *Kimanin Matanmu 300 Ne Suke Tsare A Hannun Hukuma Shugaban rundunar sojojin Nijeriya, Liyutanal Janar Tukur Buratai ya bayyana a jiya Alh...
Rating :
5