Wata majiya daga cikin mabiya shi’a ta bayyana cewar labarin da ake yadawa na mutuwar jagoransu a Jihar Kano Sheikh Muhammad Mahmoud Turi ba ingantacce ba ne, a cewarsu yana nan a raye. Har ilau, matar Ibrahim Zakzaky, Malama Zeenatu ita ma tana na raye.
Majiyar ta shaidawa Zuma Times cewar mutane da yawan sun dauka Turi ya mutu a lokacin da aka harbe shi a ciki, domin ya fadi kasa wanwar, kuma ya dade a kwance kafin a kai masa a dauki.
Dan Shi’ar wanda makusanci ne da gidan Zakzaky ya ce “Lokacin da aka harbi Turi hatta sauran ‘yau’uwa sun dauka ya yi shahada, amma da aka dauke shi zuwa asibiti, an samu nasarar cire masa harsashin, har ma wasu sun yi magana das hi.” A cewar majiyar.
A bangaren matar Zakzaky kuwa, ,majiyar ta ce a hannu ne aka harbe ta, ba kamar yadda kafafen yada labarai suka rika fadi ba.
Source Zumatimes
Title :
Yan Shi’a Sun Musanta Mutuwar Malam Turi, Zeenatu
Description : Wata majiya daga cikin mabiya shi’a ta bayyana cewar labarin da ake yadawa na mutuwar jagoransu a Jihar Kano Sheikh Muhammad Mahmoud Turi ba...
Rating :
5