Rundunar 'yan sandan da ke jihar Kaduna ta mika wasu yan kungiyar Islamic Movement mabiya akidar shi'a ga wasu jagororin kungiyar.
Wadanda aka mika din mata ne da yara da kuma wasu wadanda suka jikkata a rikicin da aka yi tsakanin Sojoji da kuma 'yan kungiyar ta Islamic Movement a Zaria.
Har yanzu dai ana kila-wa-kala game da ainihin inda shugaban kungiyar Sheikh Alzazzaky yake, kasancewar wasu rahotanni na ambaton hafsan sojin kasa na Najeriya Yusuf Buratai na cewa ba ya hannun sojoji, amma kuma bai fadi inda aka mika shi ba.
Kungiyoyin farar-hula da dama a Najeriyar ta matsa wa gwamnati lamba wajen ganin an gudanar da bincike a kan rikicin da ake zargin ya yi sanadin mutuwar mutane masu yawan gaske.
Title :
yan sanda sun saki mabiya shi`a
Description : Rundunar 'yan sandan da ke jihar Kaduna ta mika wasu yan kungiyar Islamic Movement mabiya akidar shi'a ga wasu jagororin kungiyar. ...
Rating :
5