Malam Ibrahim Muhammad Wadata, wani mai jinyar kafa, da ke zaune a gidansa da ke unguwar Rijiyar dorawa a cikin birnin Sakkwato, ya koka da yadda ’yan sanda suka jaza masa matsanancin ciwon kafa.
A ranar Lahadin da ta gabata ce Aminiya ta samu labarinsa, inda ya bayyana musabbabin wannan matsalar da ke addabarsa tsawon lokaci. “Wasu jami’an ’yan sanda ne su uku suka rika dukana da kulkinsu har suka tartse mini kashin kafa da na gwiwa a ofishin ’yan sanda na Marna, saboda taya DPO Gazali Muhammad Madugu ci mini zarafi da yake yi, don kawai rashin adalci da tunanin ban da kowa a Jihar Sakkwato.” Inji shi.Ya ce tun da dadewa DPO Gazali ya yi alkawarin sai ya sanya shi gidan yari tun da ya ki ba shi hakuri. Shi ne ya tsare shi kwana daya, ya kai shi kotun Majistare ta daya, alkali ya bayar da shi beli ganin halin da yake ciki.
“A halin da ake ciki yanzu, na rubuta takardar korafi ga Kwamishinan ’yan sanda da Kwamishinan shari’a da hukumar kwato hakkin dan Adam, don a bi mini hakkina kan walakanta ni da ci min zarafi da sanya matana biyu da ’ya’ya sha biyu da mahaifiyata cikin kunci da aka yi mini. Ni kadai ke kula da su kuma yanzu an ji mini ciwon da ba na iya tafiya ko’ina. Ga yunwa da wahala na kokarin kashe mu.” A cewar majinyacin.
Da yake bayyana wa wakilinmu takamaimai yadda al’amarin ya faru, ya ce: “A ranar 26 ga Oktoban da ya gabata ne da maraice, kanena ya same ni a kofar gidana tare da abokaina, yake gaya mini ga wani dan sanda ya zo a wurin sana’arsa ta sayar da kaya, tare da wani mutum bai san shi ba sun gaya masa matar da ya sayar wa firij ce ta yi kara ta.
“A nan take muka zo wurinsu don tafiya ofishin ’yan sanda na Marna inda aka ce an kai korafin. Da isar mu wurin aka tari mai mashin don su hau su biyu, dan sandan ya ce shi atabau bai zuwa ofis don maigidansa ne ya turo sshi kuma can za a je. Ni ko na ce masa ofis za mu tafi. A hakan muka zo shi kuma ya tafi abinsa. Da muka zo ofis ba wata maganar korafi da aka sanya tamu.” Inji shi.
Ya ci gaba da cewa: “Bayan minti talatin a ofis din, an saurari korafinmu an rubuta sai ga wannan dan sandan ya zo da mutumin da suke tare a farko. Da ya zo wurinmu yake gaya min ka ki bari na yi aikina, ka ce ba mu iya aiki ba? Sai ya wuce dakin DPO, ban san abin da ya gaya masa ba, ya fito a fusace da dan sandan, sai ya nuna ni da cewa ga shi nan. Kawai sai ya hau ni da fada, inda ya shiga ba nan yake fita ba. Ni ko na ce masa ya tsaya na yi masa bayani, ya ki bari; ya fada na fada, kawai sai ya mare ni. Sannan ya ce ni dan waye, zai iya caji na da dan Boko Haram. Ya umarci yaransa da su sanya ni a kanta, bai bar ni hakan ba ya zo shi da yaransa suka rika buguna har sai da na kai kasa. Suka dauke ni suka sanya ni sel, bayan karfe daya aka fitar da ni don ’yan uwana sun zo suna bukatar beli na. Shi ko ya rantse ba zai bayar da beli na ba sai na durkusa kasa na roke shi, tare da rubuta takardar neman yafiya. Abin da na ce ba zan yi ba ko za a kasha ni.”
Wakilinmu ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan na Jihar Sakkwato, Almustafa Sani. Ya ce bai san da labarin ba amma zai bincika. Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a samu gamsasshen bayani game da lamarin ba, domin ya ce suna cikin wani aiki mai muhimmanci.
Title :
Yan Sanda Sun Karya Kafan Wani Magidanci A Jihar Sokoto
Description : Malam Ibrahim Muhammad Wadata, wani mai jinyar kafa, da ke zaune a gidansa da ke unguwar Rijiyar dorawa a cikin birnin Sakkwato, ya koka da ...
Rating :
5