Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta yi nasarar cafke wasu mutane hudu da ake zargi da kerawa, tare da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba. Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Jigawa, Alhaji Usman Abubakar Tilli ne ya tabbatar da haka a lokacin da yake baje kolin wadanda ake zargin a gaban manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Dutse.
Kwamishina Tilli ya bayyana cewa, rundunar tasu ta yi nasarar cafke wadannan mutane ne a lokacin da dayansu mai suna Sale Muhammed daga Karamar Hukumar Birniwa ya kawo karar cewa barayi sun haura gidansa sun sace masa buhunan ridi. Ya ce bayan da jami’ansu suka binciki jikinsa, sai aka sami karamar bindiga guda daya da harsashi a tare da shi.
Ya ci gaba da cewa, “wannan dalili ya sa muka garzaya zuwa gidansa domin gudanar da bincike, inda nan take muka sake samun wasu bindigogin guda uku, wadanda ya amince cewa ya sayesu ne a wajen wani mutum mai suna Shu’aibu Adamu dan asalin kauyen Kumsa, duk a Karamar Hukumar ta Birniwa, inda shi kuma ya ce ya sami wadannan makamai ne daga wani makeri mai suna Muhammad Zailani da ke kauyen Tukuikui a Karamar Hukumar Guri a jihar.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa, bayan da bincike ya ci gaba, rundunar ta kuma cafke wasu mutane biyu, Sarki Musa da Ali Ibrahim, duk daga Karamar Hukumar ta Birniwa, inda kuma yanzu haka ana shirye-shiryen gabatar da su gaban kuliya.
Haka kuma a wani labarin, rundunar sandan ta ce ta yi nasarar cafke wasu mutane bisa zargin satar babura a yankin Karamar Hukumar Gwaram. Kwamishinan ne ya bayyana cewa, an yi nasarar cafke mutanen ne bayan an sanar da jami’an ‘yan sanda.
Ya ce, “mun sami rahoton cewa, wani mutum mai suna Usaini Alhaji Mua’azu mai shekaru 22 a Unguwar Jata Gabas, da kuma Yakubu Mu’azu mai shekaru 28, duk a garin Sara yankin Karamar Hukumar Gwaram, sun haura gidan wani mutum mai suna Mujtafa Muhammad, inda suka dauke masa farin babur dinsa kirar Jincheng mai lamba KB 372 KMC, wanda kudinsa ya kai kimanin naira dubu 95.
Ya ce bayan da aka dukufa bincike, wadanda ake zargi sun amsa laifinsu, tare da bayyana cewa makwanni uku da suka gabata, sun sato wani babur din kirar Lifan, wanda kuma shi da lamba, wanda shi kuma kudinsa ya kai kimanin naira dubu 130.
Title :
Yan Sanda Sun Cafke Masu Kera Makamai A Jigawa
Description : Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta yi nasarar cafke wasu mutane hudu da ake zargi da kerawa, tare da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba. K...
Rating :
5