A Shirin mu na wannan nan makon, munji ra'ayoyin wasu 'yan mata ne dangane da irin wankan yamman nan da suke yi domin fiya shakatawa da samarin su a cikin unguwa.
Tambayar da muka yi masu kuwa ita ce; yanzu lokacin hunturu ne, yaya suke yi da wannan dabi'a ta fita da yamma?
Yawancin 'yan matan sun bayyana cewar sanyi baya hana kwalliya, kuma sun kara da cewa a lokacin hunturu kwalliya ta fi kyau domin kuwa babu zafin ranar da zai sa su yi zufa.
A bangaren haduwa da samarin su kuwa, 'yan matan sun bayyana cewa samarin kansu sun fi son irin wannan lokaci sai dai kuma daga karshe sukan wahala domin sukan nuna juriya cikin sanyi amma daga karshe mura na iya kama su ko makamancin haka.