Wasu 'yan bindiga sun afkawa wani kauye da ke jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya inda suka kashe mutane ashirin.
Mazauna yankin, wadanda suka tabbatarwa BBC da aukuwar lamarin, sun kara da cewa mutum daya ya samu raunuka a harin, wanda aka kai a kauyen Mashema na karamar hukumar Bungudu da safiyar ranar Litinin.
Dan majalisar wakilan kasar daga yankin, Abdulmalik Zubairu, ya shaida wa wakilinmu Haruna Shehu Tangaza cewa tuni aka yi jana'izar wadanda suka mutu.
Ya kara da cewa, ''Ina ganin mun samu kusan shekara daya ba mu samu hari mai muni irin wannan ba (a wannan yankin) tun bayan wanda aka kai a kauyen Birnin Magaji.''
Daruruwan mutane ne suka mutu a cikin hare-hare irin wadannan da 'yan fashi masu satar shanu kan kai a kauyukan jihar tun somawar matsalar a shekarar 2011.
Title :
Yan bindiga sun kashe mutane 20 a Zamfara
Description : Wasu 'yan bindiga sun afkawa wani kauye da ke jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya inda suka kashe mutane ashirin. Mazauna yankin, wad...
Rating :
5