Manzon Allah (saww) ya kasance mai yawan yin Shuru. Yakan dauki lokaci mai tsawo kafin yayi magana. Kuma ba ya yin magana sai dai idan bukatar hakan ta kama.
Yana da Qarancin dariya. Kamar yadda Imamu Ahmad ya ruwaito, shi Murmushi ne yakan yi.
Yace yawaitar dariya yana kashe zuciya. Don haka yakan tsawatar da al'ummarsa daga yawan kakaci.
Ya kasance idan ya fadi wata kalma yakan maimaita sau Uku, har sai Mai jinsa ya fahimci abinda yake nufi. Kuma idan yazo gidan mutane, yakan yi Sallama. Idan basu amsa ba yakan maimaita sallamar har sau uku. (Bukhariy ne ya ruwaito). Ya kasance zancensa dalla-dalla yake yinsa. Kuma duk mai jinsa sai ya fahimceshi. Ba ya zubar zance ko surutu kamar irin yadda sauran mutane sukeyi.
Kuma duk da haka zancensa ba ya yin yawa. Idan ya zauna awaje, har zuwa sanda zai tashi, wani mai kidaya zai iya Qirga zancensa baki daya.
Shi zancensa, Zance ne mai cike da ilimi da fasaha. Duk da cewa mutanen zamaninsa masu fasaha ne, to amma basu ta'ba samun rashin fasaha acikin zancensa ba.
Yakan ce "NINE MAFI FASAHAR LARABAWA". Kuma Allah ya bashi Jawami'ul Kalim (Wato kalmomi 'Yan kadan wadanda suka tattaro maganganu masu yawa). Idan ka dauki Zancensa guda daya kace zakayi sharhi akai, to ba zaka iya Qurewa ba. Sai dai ka tsaya awajen da iliminka ya Qare.
In sha Allahu Zauren Fiqhu zai ci gaba da kawo muku tadodi da dabi'un Ma'aiki (saww) a Kullum kamar yadda aka saba.
Ya Allah yi salati da tasleemi ga Annabinka Ma'abocin Fasahar Qurewa, Mai Muryar da shi kadai ke iya magana aranar Mahashar. Tare da iyalan gidansa da Sahabbai baki daya.
DAGA ZAUREN FIQHU