Iyalan wani matashi mai kimanin shekara 36 mai suna Muhammad Abubakar da aka fi sani da Babani da yake zaune a Unguwar Kaji a garin Potiskum a Jihar Yobe suna zargin wani babban dan kasuwa mai harkar fetur a garin da hallaka shi, bayan da ya dauke zuwa Indiya don a cire kodarsa a dasa wa dansa mai suna Paris.
Marigayi Babani wanda ke da matan aure biyu da ’ya’ya tara, ya rasa ransa ne bayan da dan kasuwar mai suna Alhaji Husaini Ibrahim wanda fitaccen mai harkar man fetur ne kuma yake da gidajen mai da dama a garin Potiskum ya dauke shi zuwa kasar Indiya ba tare da sanin danginsa ba aka cire kodarsa don dasa wa dansa Paris a kasar Indiya.
Wani shakikin marigayin mai suna Alhaji Ahmad Mustapha ya bayyana wa Aminiya cewa, dan uwansu Muhammad Babani sun yi sallama da shi a ranar Talata 10 ga watan Nuwanban da ya shige cewa zai je ziyara Kaduna wurin abokinsa, to daga nan ba su sake jin labarinsa ba sai ranar 20 ga Nuwamban aka kira shi a waya da yamma cewa Alhaji Husaini Yunusa ya zo gidansu da kannensa biyu shi ne sai ya tafi gidan.
Ya ce, “Bayan da na je gidan sai na tarar da Alhaji Husaini zaune a falon malaminmu shi da wasu mutum hudu da ya zo da su. Sai Alhaji Husaini ya tambaye ni ko ina da labarin Babani? Na ce lallai ina da labarinsa, don ya ce min ya yi tafiya zuwa Kaduna. Sai Alhaji Husaini ya ce kanenku tafiyarsa ta yi nisa don ya bar Najeriya zuwa kasar Indiya. Sai na ce kamar yaya? Sai ya ce ai Babani sun tafi da ’ya’yansa biyar zuwa kasar Indiya domin akwai dansa marar lafiya mai suna Paris da ke da ciwon koda da nufin Muhammadu (Babani) ya amince a ciri kodarsa a dasa wa Paris a matsayin taimako.”
Alhaji Ahmadu ya kara da cewa da ya ji haka, sai ya tambayi Alhaji Husaini cewa, yaya aka yi haka ba tare da sanin kowa ba? “Mu ga abin da ya fada mana cewa za shi Kaduna ne ziyara,” inji shi. A nan sai Alhaji Husaini ya ce shi Muhammadu Babanin ne ya ce kada su fada wa kowa, shi ne suka rufe maganar ba su fada wa kowa ba suka yi tafiyarsu kasar ta Indiya har haka ta kasance. Da suka tafi kasar Indiya da kwana takwas don ba da kodar ne sai kuma Allah Ya yi masa cikawa. A nan sai na ce to yaya za a yi a ce an tafi da shi kasar Indiya don ya ba da koda ba tare da sanin ’yan uwansa ba, ai wannan zance ne kawai babu maganar taimako tunda ba dan uwansa ba ne ba kuma danginsa ba ne, sai dai inda kudi kuka rude shi,” inji Alhaji Ahmad.
Ya kara da cewa bayan mako daya a ranar Alhamis aka kawo musu gawarsa garin Potiskum, sai suka je caji ofis inda DPO na Potiskum ya sa aka dauki jawabinmu da na Alhaji Husaini sai ’yan sanda suka ce a sa shi Alhaji Husaini a bayan kanta. Daga bisani sai DPO ya sa a gwada gawar don sanin ainihin abin da ya faru. “Kuma daga nan sai muka tafi Damaturu wajen Kwamishinan ’Yan sanda, amma sai muka ga Kwamishinan yana jan kafa a kan wannan abu. Saboda muna ganin Alhaji Husainin na gadara da dukiya, kuma ana cikin haka ne sai wani daga cikin ’ya’yan Alhaji Husainin ya ce mu yi hakuri mu je gida za mu sasanta a kuma yi jana’izar marigayin. To wannan abu shi ya faru don haka mu ’yan uwan marigayi Muhammad Babani ba mu yarda da wannan abu na rasuwar dan uwanmu ba a hannunsu ba, kuma muna fata hukuma za ta bi mana hakkinmu,” inji Alhaji Ahmad.
Da Aminiya ta tuntubi Alhaji Husaini Ibrahim mahaifin Paris matashin da ke fama da jinyar koda har aka tafi da marigayin kasar Indiya don cire tasa, dangane da wannan zargi da ’yan uwan marigayi Babani ke yi cewa ya dauki dansu zuwa kasar Indiya ba da saninsu ko amincewarsu ba kuma ya rasu a can? Sai ya ce, ya san zai mutu ya gamu da Allah, amma a iya saninsa ya san marigayin da kansa ya tafi Kano lokacin da dansa Paris na kwance a asibiti a Kano yana jinya, da ya je ganinsa sai ya ce wa Paris tunda ciwon koda ne ke damunka in zai yiwu zan ba ka tawa kodar guda daya, sai ya ce to in har za ka ba ni ai yana da kyau.
Alhaji Hussaini Yunusa wanda fitaccen mai harkan man fetur ne da gidajen mai a garin Potiskum kuma ya kara da cewa, sai marigayin ya ce wa dan nasa to amm a ya ba shi lokaci, to bayan wata biyar sai marigayin ya sake dawowa wajen Paris ya ce masa, ya shirya yanzu zai ba shi koda, sai Paris ya ce masa to bari ya fada wa mahaifina. Sai marigayi Babani ya ce in zai fada to ya fasa don sai a yi ta gulmarsa a ce ya karbi kudi ya sayar da kodarsa.
Alhaji Husaini Yunusa ya ce, “Haka aka rika rufa-rufa don kada in sani, saboda in har na sani dole sai
na tuntubi iyalensa kafin a tafi da shi, amma duk haka na yi ta matsa lamba a kan sai an sanar da iyalensa amma marigayin ya kekasa kasa ya ce in har sai an fada wa ’yan uwansa to shi zai fasa taimakawa, haka aka yi ta fama daga karshe suka je suka yi biza suka hau jirgi suka tafi kasar Indiya. Bayan su isa kasar Indiya ne da kwana daya tun kafin a yi aiki aka yiwo masa waya cewa, Muhammad Babani ya rasu. To ka ga ba a ma ciri kodar ba Allah Ya yi masa rasuwa.”
Ya ce yanzu haka mahaifiyar dan nawa tana shirye-shiryen tafiyar kasar Indiya don ba da koda ga danta. Wannan shi ne gaskiyar magana.
Da Aminiya ta tuntubi Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Yobe, Alhaji Muhammad Zanna Ibrahim a kan lamarin, sai ya ce, wannan magana tana nan a hannun jami’an bincike tukunna.
Title :
Yadda dan kasuwa ya hallaka matashi wajen cire kodarsa don dasa wa dansa
Description : Iyalan wani matashi mai kimanin shekara 36 mai suna Muhammad Abubakar da aka fi sani da Babani da yake zaune a Unguwar Kaji a garin Potiskum...
Rating :
5