Ashe bai gama ganin komai ba tukuna. An
shrya zeenah a gdn iyaynta, aka fito da ita domin
sallatar gawar. Alh. Mu'azu da 'ya'ynsa tare da
jama'arsu na kofar gida suna zaman jira, ana fito
da ita suka taso don bin sahu. Alh. Zubairu yace
sam basu isa ba! Mamaki ya ishi kowa, liman
yace, "me ya kawo wannan tashn hnkalin a gaban
gawa?" alh. Zubairu yace, "Allah gafarta malam
su suka kasheta, menene na zuwa sallatar ta?"
liman yace, "wannan ba gaskiya bace, domin
baka da wata shaidar da zata tabbatar da zargn
da kake yi. A shari'ance kuma mijnta yafi ka iko
da ita. Sbd haka ba grmanka bane irin wannan
jahilcn ka tsaya gaban gawa kana maganganun
da basu dace ba". Ya nuna su munnir ya ci gaba,
"ku wuce kubi sahu, idan kuma hanasu nima
gaba nayi, don ba'a gabana za'a yi wannan
mummunan aikn ba". Jikn alh. Zubairu yayi
sanyi, bai be kala ba har st alh. Mu'azu suka
jeru, liman yai kabbarar sallah. Munnir tsaye
kawai yake, amma ilahirn jiknsa babu abnda ke
aiki, sbd tsabar juyayn irin wulakncn da alh.
Zubairu ya dade yana yi musu. A yau kuma ya
tabbatar da alh. Zubairu zai iya halaka shi sbd
kiyayya. Baya haufi akan zancn mahaifnsa da
yace babu mamaki shi aka zo kashewa, tsautsayn
ya fada kan zeenah, da yake ita ce mai kararrn
kwana. Duhu ya mamaye idnsa, kunnuwnsa suka
dode, gaba daya kwakwlwrsa ta hargitse da wani
sauti da bai taba jin irnsa ba. Bai san lokacn da
ya ynke jiki ya fadi a sume ba, daidai lokacn
liman yana sallamewa daga kabbarorn sallar
jana'iza. Hnkaln jama'a ya koma kan munnir, nan
da nan aka dauke shi zuwa faln baki da kofarshi
ke bude daga waje. Nan alh. Mu'azu ya barsu da
yayansa, shi yabi 'yan kai gawa a motrsa. Ko a
makabrtar ma yana gefe a tsaye aka gama komai,
bai matsa kusa da kabarn ba don gudun tashn
hnkali. Daga nan inda yake yayi mata addu'a,
hawaye suka zubo masa, ya share ya koma
motarsa yabi tawaga suka dawo gida.
Munnir dai na kwance rai ga hannun Allah,
don kuwa bai farfado ba duk iya dabarnsu. A
haka suka sashi a mota suka kai asibitin kudi
dake kusa dasu. Take nan aka bashi gado aka
daura masa karin ruwa. Hnkaln kowa ya tashi,
musamman iyaynsa, da zarar suka dubeshi, suka
dubi 'yar jaririyar dake hannunsu, suka kuma tuna
mahaifyrta, sabn kuka ke zuwa musu sbd tausayi.
Har dare munnir bashi ckn hayyacnsa, wai bai
farfado bane? Wai duniyar ce tayi masa daurin
goro? Wnda gashi yana kalln mutane amma baya
iya amsa gaisuwarsu. Can ckn zcyrsa kuwa
azabar ciwo take masa, shi kadai zai iya fadin
ynda yake ji. Zeenah ta tafi ta barshi da 'yar
jaririya da yake ganin ta ma fishi bukatar zeenar
da matsaynta na mahaifya a gareta watau UWA!
Wacce Allah ya ratayawa duk wani jin dadinta a
wuynta, ta yadda ko da tana da rai idan bata tare
da babnsa jin dadnta ragagge ne, komai gatan da
take dashi a gdn kuwa, balle wannan da babu
rayuwar gaba daya. Lallai wannan jaririya abar
tausayi ce. Tabbas wadanda suka aikata wannan
mummunan aikn sun cutar dashi ba kadan ba,
kuma koda wannan alhakn kadai ya barsu hakika
Allah ba zai kyale ba. Sai dai duk da irn tsananin
tunanin da yake ciki, bai fidda masa imanin cewa
kwanan zeenah ne suka kare ba, duk iya
dabarnsa bai isa ya kara mata ko da dakika daya
ba. Haka ya kwana a asibit rayuwa babu dadi. A
yayin da ake ci gaba da amsar gaisu a duka
gidajn biyu. Babu wnda mutuwr zeenah bata
grgiza ba, haka kuma kowa ya budi baki alheri
yake fada game da rayuwar zeenah a dorn kasa.
Don ko lokcn da ake badakalar auranta da munnir
kowa yasa alh. Zubairu yayi son zcya, sbd haka
kowa yake mata kyakkyawn zato tare da fatan
Allah ya tona asirin wadanda suka aikata wannan
aika-aika.
Karfe 10 ta wuce lokcn da munnir ke zaune
bisa gado duk ya jeme, yayi wata mummunar
rama tashi guda. Abdullahi ke ta rarrashnsa yana
bashi baki akan yayi kokarn sa wa cknsa wani
abu. Zuru kawai yayi. Yayan nasa ba zai gane
amsar ba, ta ina abncn zai wuce? Ya karkada kai
idanuwa tam da kwallah, yasa hannu ya karbi
kofin tea daga hannun yayan nasa. Kurba daya
ya yiwa tin aka budo kofar dakin, matashin da ya
sawo kai ck n dakn suna da kamanni da munnir
kwarai da gaske, ka rantse da Allah uwarsu daya
ubnsu daya. Ckn sassarfa ya nufo inda munnir
din ke zaune, wnda tuni idanuwnsa suka canza
launi, fuskrsa ta kara dagulewa. Zama kawai yayi
bakn gadn, bai iya cewa komai ba ya shiga
shatatar hawaye, hakn ya sa munnir zubda nasa
ruwan idon ba kadan ba. Abdullahi ya kama
kafadrsa yace, "haba nura, kai da zaka rarrashe
shi sai kuma ka tasa shi kana naka kukan? Ai
addu'a ya kamata kuyi mata. Don Allah kayi
hakuri ka dake zcyrka, domin kai ne mutm na
karshe da muke sa ran zai iya kwntarwa munnir
da hankali". Yayi iya kokarnsa don ganin ya
tsaida hawayn, amma ya kasa sbd tsabar
tausayn abnda ya sami aboknsa. Munnir da
kansa ya koma yana bashi hakuri. Gaba dayansu
suna ta sharar kwalla. Abdullai dai fita yayi ya
basu guri. Nura ke fadin, "ban fa yarda ba munnir
tun lokacn da abba ya kira waya ya gaya min.
Haka kawai, ko tausayn 'yar jaririyar da ke
gabnta ba'a ji ba? Koda muka shiga kdna sai da
tace mu dai biya ta gdnku din mu gani. Amma
wlh duk da haka bamu yarda ba, sai da muka iso
muka ga taron jama'a. Kai inna-lillahi-wa-inna
ilaihir-raji'un! Munnir ka ga tashin hnkali" ya
girgiza kai ya goge kwalla, sannan yace, "ba'a
cewa komai nura, ni kaina ganin abin nake tamkr
almara. Kuma gaba daya tunani na ya kare wajen
sanhn WA YA KASHE TA?
Ya sauke wawan numfashi yace, "ita ce ai
tambyar, kuma abba yace ba'a dauki komai ba a
gidn. Kaga hakan ya tabbatar da kisan ya kawo
su kawai". Sun kwashe mintoci tsit! Babu wnda
ya kara wani abu, nura yasa hannu ya daulo kofin
tin da munnir ya aje ya mika masa, "ungo kasha
munnir ko kaji karfn jiknka" yace, "aje shi nan
kawai nura...." "bai fa yuwuwa munnir, dole ka ci
abnci. Ina son ka sani, wannan rabuwar taka da
zeenah ba irin waccan ta baya bace wacce ta
hana maka barci da cin abnci. Ita wannan iyakar
soyayyarka da ita kawai addu'a, don abnda tafi
bukata kenan". Wani dan sirirn kwalla ya gangaro
bisa kuncnsa, nura ya kera matsoshi sosai ya
kama hannunsa ya damka masa kofin, "daure ka
kwalkwale kawai". Ya amsa ya kafa kai. Ya
shanye ne dai kawai amma bai ji dandanonsa ba
balle har yayi masa maganin yunwr da yake ji a
halin ynyu, wacce ya tabbtar bata abinci bace.
Saidai samun kusa dashi ya dan taimaka masa
rage wasu tunane-tunanen. Sun dauki lokaci
munnir yana maida masa irn ruwan masifar da
alh. Zubairu yake yayyafawa tun jiya. Har akayi
sadakar uku munnir na gadn asibiti sbd jininsa da
yayi mugun hawa, bai sauka ynda ake so ba,
kuma likita na tsorn sallamarsa a hakan. Jama'a
da dama nan suke zuwa gaisheshi tare da yi
masa gaisuwa. 'Yan-sandan da ke tare dashi a
haln ynzu ckn fararen kayu sune jami'an binciken
da aka damkawa alhakn hano wadnda suka kashe
zeenah. Tambayoyn har sun ginshi munnir, baya
so amsawa
A halin ynzu badakalar da aka sha kafn
tabbatuwar aurensu shi 'yan-sanda ke son sani,
domin tuni suka fahmci babu jituwa tsakanin
surukan biyu. Ckn kosawa munnir ya dubi
insifekta yace, "bana jin rikicin gidajenmu na da
alaka da kisan zeenah. To a ciki wa zai kasheta?
Babanta? Ban jin alh. Zai sa a kashe zeenah 'yar
cknsa kuma tilo daya mallaka, don kawai baya
son auranmu. Mijin da aka aura mata kuwa taki
zama dan-uwanta ne, kuma tun rabuwarsu
abbansa ya raba shi da garin nan. Ni dai bana
zargn kowa illa bata-gari". Su dai suna son jin
wace badakala aka yi (ah, ai muma muna son
sani, inji siyya ko ya kuka ce 6tas?), watakila su
zakulo wasu abubuwn da zasu taimaka wajen
binciknsu. Munniri baya son TUNA BAYA (hehehe,
na takori inji siyya), hasali ma bai son surutn yayi
yawa a haln da yake ciki ynzu. Don haka ya koma
da baya ya jingina da filo hannaynsa rungume da
krjnsa, idanuwnsa suka jirkita. Nura ke ta
rarrashnsa, "munnir ka taimaka ka basu labarin
nan tnda suna son jin sa, wata kila ya taimaka
musu samun wasu bayanan. Ka sani fa har ynzu
alh. bai daina ruwan masifa ba da zargn ku kuka
kashe masa 'ya". Munnir ya dubeshi ido cike da
kwalla yace, "don Allah ka bar daka ta wannan
mutumin, idan yaso ma yasa a daure ni. Wlh a
shrye nake da in karasa rayuwata a gidn yari. Sai
me?". Insifekta umar yace, "duk wannan maganar
ma bata taso ba, amma abnda na lura, kai
munnir baka son ka bamu hadin kai, wnda hakan
sabawa shari'a ne, ko da kuwa ka yafe a
matsaynka na mijnta, hakkin hukuma ne tayi
bincike don gano bata garin da suke aikata irin
wadannan mugayn laifuka. Sbd haka wajibin ka
ne ka wajibnka ne ka warware mana zare da
abawa, don ci gaba da bincikenmu" Insifekta sani
ya karbe, "to wai menene a labarin da kake
boyewa baka son a sanshi? Ina son ka fahmci
wani abu, ba fa zamu kyaleka ba akan case din
nan, sbd kaine jigo kuma shakikn zeenah, wnda
ya kamata mu sami bayanin komai da ya
shafeta" "gaskya ne, wannan magana haka take"
inji nura. Munnir ya numfasai. Kai sun matsa
masa da yawa. Fuska a yamutse yake fadin, "naji
naji....." yayi dan shiru ido runtse, jim! Sannan ya
bude!*********
Mahaifina alh. Mu'azu shika haifaffn
garin shika ne, wani gari idan ka wuce zariya
bisa hnyar zuwa funtuwa. Gaba daya zuriyarmu a
can suke, kuma zumuncnmu yana tfya ynda ya
kamata duk da cewar shi kadai ne ya rage babba
ckn gdnsu a ynzu, ma'ana iyaye da sauran yan-
uwan haihuwarsa duk sun koma ga ubngiji.
Karatn allo ya fara kawo shi zrya, a lokacn yana
dan kimanin shekaru 10, har ya fara makarntar
boko a can. Yana aji uku na firamare mahaifnsu
yabi shawar aboknsa suka cire yarnsu suka turo
su karatn allo. Ba karamin ciwo abn yayi wa
babana ba, sai dai ilimin addini ya zama dole a
neme shi, wnda ya zama wajibi a turo su karatn
allo, domin zamaninsu babu wadatar islamiyoyi a
ckn gari. Ya ci gaba da karatu tukuru a hannun
malaman su, amma kwarai ransa ke sha'awar
karatn zamani. Shi yasa da gamansa shekaru 14
yasa kansa makarntar boko ta (NURUL HUDA T/
WADA ZARIA). Da farko malaminsu bai amince
ba, sbd haka ya aikawa kakanmu yazo. Ganin
yadda babana ke kuka yana rokn a kyale shi ya
hada da kartn boko, shi yasa mahaifnsa ya
amince masa, ya kuma ba malaminsu umarnin a
kyale shi kawai. Kakanmu bai baro zariya ba sai
da ya cika masa jaka da littafai da sauran
abubuwn bukatar makarntar boko, sannan da
kansa ya sake daukarsa ya kashi gabn
hedimasta. Da aji biyar ya fara, sannu ag hankali
ya kammala fisamare ya fada sakandire. Kamar
wasa karatu yayi zurfi, yaynda ta fannin
muhammadiyya ya jima da saukewa, tilawa kawai
yake tare da daukar wasu darussa na ckn wasu
litattafan. Kammala sakandirnsa ke da wuya
mahaifnsu ya rasu, a lokacn yana zaman jiran
sakamakn jarabawarsa, kuma burinsa kawai ya
fada jami'a, sai yaga abnda ya ture wa buzu nadi,
amma Allah bai nufa ba. Rasuwr mahfnsu ya
rushe masa komai, dole ya koma shika bisa
umarnin 'yan uwansa, suka fada noma gadan-
gadn a gonar gadn mahaifnsu.
Shekaru 5 tsakani akayi masa aure da
mahaifiyarmu, 'yar babbar gida, don mahaifnta
shi ke limancn masallacn juma'a. Tun daga lokcn
ya fada fafutukr nema. Da yake yana da kokari
sosai, sam baida son jiki. Duk kasuwannin
kauyukan nan na kewayn zariya babu wacce baya
zuwa, wani lokcn ya kai amfanin gona, wani
karon kuma dabbobi. Allah yace tashi in taimake
ka. Tabbas Allah ya taimaki baba, domin mun
taso ni da yayana Abdullahi ckn jin dadn rayuwar
duniya. Ba zan sanya shi ckn jiga-jigan masu
kudi ba, amma kwarai babanmu yana daya daga
ckn masu kudin unguwar t/wadan zariya, inda
muka taso muka tsinci kanmu ckn kayataccn
gdnsa na zamani, domin tun ban zo duniya ba ya
baro shika, kasancewar tsakanin haihuwata da ta
yayana Abdullahi shekaru 8 ne. Munyi karatu a
makarntar 'ya'yan gata a wancan lokacn, wacce
ta kasance tilo a fadin zariya, sai dan wane da
wane, watau (Therbow School), hakan kuwa ya
samu ne sbd son ilimi da bashi mahimmnci irin
na mahaifnmu, domin baya ga mu ma, babanmu
ya dauki nauyn karatn yara da yawa ckn 'ya'yan
'yan-uwnsa da ma na makwbta da abokan arziki.
Nasan zaku sha mamaki idan nace muku
mahaifinmu sai da yayi digiri a fannin kasuwnci,
duk da cewar baya kwadayn aikn gwamnati, yafi
sha'awar kasuwncnsa. Kuma ina ganin tabbas
wannan ilimi shi yake kara masa haske a duk
inda yasa gaba. Hakika mun gode wa Allah,
domin mun samu gata ta kowacce fuska, ilimin
addini da tarbiyya ta gari, shi yasa muka taso
gwanin sha'awa ga kowa. Gidan alh. Zubairu
mahaifn zeena shi ke kallon namu, kuma a haka
muka yi wayau muka gansu, tamkar ynda shagon
sa ke daura da shagunan babanmu biyu a
kasuwar sabon gari. A tunaninmu zai iya
kasancewa abokai ne, sbd makwabtakar dake
tsakaninsu gida da kasuwa, amma abnda muka
fahmta daga baya, alh. Zubairu baya son muna
shiga gdnsa.
Duk lokacn da ya riskemu ckn gdnsa tare da
zeenah muna wasa a guje yake biyomu ya koro
mu waje. Sai dai kun san yarnta, hakan bai hana
mu shiga gobe ba, kar ma ni inji labari, ko don
yaya abdullahi ya fini sanin ciwn kansa ne? Don
ni kam sai dai in ban so shiga ba, shigewa nake
muyi ta wasa da ZEENAH.! Kuma umma (maman
zeenah) bata cewa komai, har ka kan bamu duk
abnda take dashi na kwalamar yara. Amma ita
zeenah babu ynda za'ayi ta shigo namu gdn, ko
nace tazo muje gdnmu sai tace babnta zai yi
mata shegn duk. To menene dalili? Zeenar kanta
bata sani ba, balle ni, sbd sau da yawa ina
tmbayar baba da mama, sai suce babu komai, mu
dai rinka gaishe shi duk inda muka ganshi. To ko
mun gaishe shi baya kallnmu balle ya amsa.
Hakan bai sa mun fasa ba. Ni kam har oyoyo
nake zuwa yi masa na taya zeenah idan ya dawo
daga kasuwa da yamma. Tamkar bai sanni ba
haka yake yi, ya kama hannun 'yarsa su wuce
ckn gida. Wata rana bana mantawa ya biyoni da
gudu na fadi a zaurn gdn, baki na ya tokari
siminti sai jini! Na fasa kuka na kasa tashi. Kaina
ya tsaya ya lullubeni da masifa, "Allah ya kara,
maran kunyan banza da na wofi! Yaro kamar
bakin maye, kullum sai na koreka gidana amma
sai ka dawo! Dama shigiyar kafar ta karye kowa
ya huta, fitinannen yaro mara mutnci irin
UBANSA! To zan gani in akwai kwndalar ubanka a
ckn tubalin gidn nan. Tashi ka fice min da gani".
Muryar umman zeenah naji tana fadin, "haba alh.!
Wannan abu da me yayi kama? Ace har kullm ba
zaka daina fada da yara ba? Ai bai dace ba ma
fadnku ya rika shifar yara, shi yaro me ya sani?"
tasa hannu ta dago ni, jini taga ya wanke min jiki,
hnkalnta ya kara tashi, "sbd Allah ina amfanin
haka? Dubi fa?" yace, "ki tsinke ni da mari ne sai
ki tabbatar min kin fini sanin ya kamata!
Mtswww...." ya ja dogn tsaki ya wuce ckn gida.
Ta jawo ni tana rarrashi har ckn gdn, ta cire min
kayan jikina ta wanke ni fes! Ina tsaye lebena a
kumbure, zeenah nata kallona kamar tayi kuka.
Umma ta gama rubutun da take yi a 'yar takarda,
ta miko min tace in kaiwa mama. Ta bani rigata
da biskit ta rako ni zaure.
Ina shiga gida yaya abdlhi na zaune kofar
daki, shi ya fara tmbayata, "ina kaji ciwo?
Faduwa kayi? Mama zo ki ga bakin munnur" Ta
fito da saurnta, tayi tsaye tana duba na, "ynzu
sbd Allah ina kaje ka faso baki haka? Kai baka ji
ko?" idanuwana suka kawo kwalla, nace, "baban
zeenah ne ya......" fallamin marin da tayi sai da
jiri ya kwasheni nayi faduwar 'yan bori, fitsari ya
kubce min sbd azabar da naji bata misaltuwa. Na
saki rigar dake hannuna da biskit da takardar, na
tsandara ihu, duk da haka mama bata tausaya
min ba, hnkalnta a tashe ta kama min kunne ta
daka min tsawa, "gdn alh. Zubairu gdn ubanka
ne? Nace gdn ubnka ne?" ilahirn jikina ba inda
baya rawa, ina kuka ina fadin, "a'a, a'a......" ta
sake tika min dundu tsakar baya, "to me kake
nema a gdn nan da kullm sai ka shiga? Kaga
yayanka ya shiga ne? Iye? Watau kai baka san
zuru ba ko?". Ta kuma cira hannu zata kara min,
ckn gudunmawar Ubangiji sai ga babana, tun kafn
ya karaso yake cewa, "menene? Me yayi kike
jibgar min shi haka?" Haba! Ina jin muryarsa na
mike da gudu na nufi gunsa, amma duk da haka
sai da mama ta sake make ni, sbd takaicn da na
cusa mata. Ni kaina nasan bakn cki ne yasa ta
rufeni da dukan. Ganin bakina a suntume yasa
baba ya hau fada, "sbd Allah me yasa haka? Don
ranki ya baci sai kuma ke nemi nakasa min yaro,
baki lura da inda zaki buge shi!" ta nuno ni tana
haka, "kana zatn ni na fasa masa baki ko? To
tambayeshi inda yaje aka kusan nakasa mak kusan nakasa mak a
shi. Ba dai kace babu ruwan yara a harkarku ba
ko? Kaki raba su da gdn nan, kullum sai an koro
maka yara baya damunka, gara wannan shi baya
zuwa, amma wanna sokon da bai san inda ke
masa ciwo ba, ko da yaushe yana gidan. Ga irnta
nan, duk ran da ya karyashi kai dashi kunyi
karatn ta natsu". Ta wuce da sauri ta fada daki.
Baba ya dago fuskata ya kare min kallo, sannan
ya dafa kaina yace, "yi shiru, zo muje ka sauya
kaya, in kaika kemis". Nasa hannu na share
hawaye, ya kamoni zai wuce dani daki, na wuce
da sauri na kwaso takardar da biskit din da umma
ta bani na mika masa, ya karba yace, "na
menene?" nace umma ce ta bani tacei in kawo
mama takardar". Ya warware ya karnta, "DON
GIRMAN ALLAH MAMAN MUNNIR KIYI HAKURI.
HAKA KUMA KI BA BABANSA HAKURI, HAR GA
ALLAH RAINA BAYA SON ABNDA KE FARUWA, SAI
DAI MUYI ADDU'A ALLAH YA KAWO KASHN
WANNAN AL'AMARIN".