Assalamu alaikum.
ZAUREN FIQHU ya rubuto wannan nasihar ne sakamakon yawan wasikun da muke samu daga Matasa Maza da mata, suna neman taimako akan illolin da suka samu ajikkunansu. sakamakon Istimna'i wato Masturbation.
Shi dai masturbation (Istimna'i) shine sanya da hannunka ko kuma wani abu mai kama da haka, ajikin al'aurarka domin biya m\ kanka bukatar sha'awar dake tare dakai. Maza suna yi, Mata ma suna yi.
Wannan harkar, Mu anan ZAUREN FIQHU munyi bayani akanta yafi sau ASHIRIN. Mun kawo hujjoji gamsassu daga Alqur'ani da Sunnar Ma'aikin Allah (saww) da fatawoyin Amintattun Malamai duk akan HARAMCIN ISTIMNA'I. Amma duk da haka wasu matasan basu yarda sun dena ba. Wasu kuwa sunji tsoron ALLAH sun riga sun dena. Kuma sun tuba zuwa ga Allah.
Babban dalilin da yake janyo musu afkawa cikin wannan bala'in shine :
1. Kallon Fina-finan batsa.
2. Shiga shafukan internet na batsa.
3. Yin zantukan batsa tsakanin saurayi da budurwa.
4. Kusantar zina ta hanyar kallo da shafa, ko zance da dai sauransu.
5. Chatting din batsa, Shiga group na 'Yan batsa, etc.
Wasu kuma suna aikata hakan ne don gudun afkawa ZINA, basu san cewa shi dinma ZINAR bane!!
Istimna'i bashi yiwuwa sai kanayi kana tunanin kamar gaka nan (ko kuma gaki nan) kana aikata haramtaccen Jima'i da wani ko wata.
Idan kun Qi bari domin Allah, to ku dubi irin illolin da yake haifar muku ajikinku mana!!!
1.MUTUWAR IDANU.
2. MUTUWAR AL'AURA.
3. CIWON BAYA.
4. BUGAWAR QIRJI.
5. RIKICEWAR TUNANI.
6. YAWAN MANTUWA.
7. QARANCIN 'YA'YAN MANIYYI.
8. SAURIN INZALI.
9. CIWON SANYI.
10. KANKANCEWAR GABA.
11. TOSHEWAR BASIRA.
12. SHAFAR ALJANU, ETC.
Wadannan 'yan kadan ne daga cikin Matsalolin da ISTIMNA'I yake haifarwa. kuma duk wanda bqi tuba ya dena ba, idan ya mutu ahaka zai je ya tarar da hisabi.
DON GIRMAN ALLAH!! Matasa ku kiyayi zina da duk dangoginta. ku kaurace ma duk wani abinda zai rika motsa muku sha'awa. Idan da hali kuje kuyi aure. idan kuma babu hali, to ku yawaita azumi.
ALLAH YA SAWWAKE.
Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA, DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM, WHATSAPP, da sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.
Manzon Allah (saww) yace: "WALLAHI IDAN ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA, YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
DAGA ZAUREN FIQHU.
Munyi wannan rubutun ne aranar 30 ga watan January na 2015. Da misalin Qarfe 7:37 na safe. Kuma yawan mutanen da post din ya kai zuwa garesu 52,944.
Amma duk da haka an samu wasu Shaitanun Mutane sun kwafi rubutun, sun Kankare wasu kalmomin sannan sun Qara Son ransu aciki.
Masu yin haka, Don girman Allah ku dena.
Title :
Wasika Zuwa Ga Masu Masturbation [ Istimna'i]
Description : Assalamu alaikum. ZAUREN FIQHU ya rubuto wannan nasihar ne sakamakon yawan wasikun da muke samu daga Matasa Maza da mata, suna neman taimak...
Rating :
5