Rahotanni daga jihar Kaduna sun rawaito cewa wasu mafusatan matasa sun yi wa fitaccen jarumin finafinan Hausan nan Adam A. Zango ruwan duwatsu tare da ihun 'ba ma so' a yayin da aka gabatar da shi a wurin kalankuwar mawaka da aka gudanar a filin wasan kwallon kafa na Ahmadu Bello da ke Kaduna a jiya.
Majiyarmu ta gano cewa matasan sun yi wa jarumin haka ne sakamakon furucin da ya yi na cewa shi koyawa matasan Kaduna yadda ake shigar gayu.
An dauki tsawon lokaci kafin jami'an tsaro su shawo kan mafusatan matasan. Inda suka nemi Zango da ya nemi gafararsu kan kalaman nasa.
Daga bisani dai mawaki Dauda Kahutu Rarara ne ya zo ya baiwa jama'ar da ke wurin hakuri kafin daga bisani aka baiwa Zango dama ya gabatar da tasa wakar.
Taron mawakan ya kuma samu halartar mawakan Turanci irin su, Olu Maintain, Wande Coal, Patoranking da MI. Sannan kuma fitaccen mawakin Amurka, Jo da Tuface na Nijeriya suna daga cikin wadanda za su gudanar da wasa a yau.
Bankunan Zenith, Sky da kamfanin sadarwa na Etisalat su suka dauki nauyin gudanar da bikin. Sannan kuma shugaba Muhammadu Buhari shi ya bude bikin a jiya, inda za a kammala shi a yau.
Rariya
Title :
[Updated] An Yi Wa Adam A. Zango Ruwan Duwatsu A Wurin Taron Mawaka A Kaduna
Description : Rahotanni daga jihar Kaduna sun rawaito cewa wasu mafusatan matasa sun yi wa fitaccen jarumin finafinan Hausan nan Adam A. Zango ruwan duwat...
Rating :
5