Rahotanni daga Yemen na cewa tsohon Dogarin Osama Bin Laden, Nasser Al Bahri ya rasu bayan ya sha fama da jinya.
Wasu majiyoyi sun shaida wa BBC cewa tsohon Dogarin, wanda ake wa lakabi da Abu Jandal ya rasu ne a wani asibiti a garin Mukalla da ke kudancin Yemen.
Al Bahri Dogari ne, harwayau Direba ga Osama Bin Laden, wato shugaban kungiyar Alka'ida mai hedikwata a Afghanistan.
Abu Jandal dai ya koma Yemen ne a shekara ta 2008 bayan an sake shi daga sansanin Guantanamo.
Tsohon Dogarin Osama Bin Laden din dai na daga cikin mayakan Alka'eedah da suka kai hare-hare a 1990 da 'yan kai a kasashen Bosnia da Somalia da kuma Afghanistan.
Title :
Tsohon Dogarin Osama Bin Laden ya rasu
Description : Rahotanni daga Yemen na cewa tsohon Dogarin Osama Bin Laden, Nasser Al Bahri ya rasu bayan ya sha fama da jinya. Wasu majiyoyi sun shaida w...
Rating :
5