Abdul Haruna, wani dan wasan kwallo dake buga ma Kano Pillars ya fadi ya mutu a lokacin da suke wasa da wata kungiyar kwallon kafa.
Dan shekara 27, Haruna ya fadi ne a lokacin da ake buga wani wasan zumunta.
Inda yake magantawa akan lamarin, Manajan Kungiyar Ideis Malikswa ya bayyana cewa sun girgiza akan abunda ya faru.
Yace: “Muna wasa da wani karamin kungiyar kwallon kafa. Kawai sai Haruna ya fadi ya rasu. Kafin rasuwar Haruna ya samu kwantiragi da wata kungiyar wasan kwallo dake kasar Vietnam. Ya rasu ya bar matar shi wadda ya aure a 2012 kuma sannan suna da ‘Da guda Daya.”
Title :
Tsohon Dan Wasan Kano Pillars Ya Rasu
Description : Abdul Haruna, wani dan wasan kwallo dake buga ma Kano Pillars ya fadi ya mutu a lokacin da suke wasa da wata kungiyar kwallon kafa. Dan she...
Rating :
5