-Sanata Shehu Sani
Sanata mai wakiltar Kaduna ta Arewa a Jiyhar Kaduna, Sanata Shehu Sani, ya yi tir da taron ruguntsimin mawakan kasar nan da aka shirya yi a Kaduna. Shehu Sani ya ce wannan la’anannen taro ne, kuma bai yi daidai da dabi’un mazabar da yake wakilta ba, da jihar Kaduna da ma Arewa baki daya.
Bugu da kari, ya ce abin haushi da takaici ne a ce za a shirya wannan taro a Kaduna a daidai lokacin da arewa ke zaman makoki da kuncin ragargaza yankin da Boko Haram ta yi, inda ya ce an kashe mutane sama da dubu ashirin da biyar, ga milyoyin da suka rasa gidaje sannan kuma ga dubban wadanda aka arce da su aka yi garkuwa da su.
Sanatan, wanda ba ya iya gani ya yi shiru, ya ce irin kaifin matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita kawai ta isa duk mai hankali kada ma ya yi tunanin kada ma ya tara jama’a a yi wannan sharholiya. Ya ce ma’aikata da masu karbar fansho na fama da kiki-kakar biyan su hakkinsu, don me wani zai kafci kudi ya shirya taron sharholiya?
A karshe ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya nisanta kansa daga taron ta hanyar kin amsa gayyatar da aka yi masa.
Title :
Tir Da Ruguntsumin Mawaka Da Za A Yi A Kaduna-Shehu Sani
Description : -Sanata Shehu Sani Sanata mai wakiltar Kaduna ta Arewa a Jiyhar Kaduna, Sanata Shehu Sani, ya yi tir da taron ruguntsimin mawakan kasar nan...
Rating :
5