Gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji Umaru Tanko Al-Makura, ya bayar da umarnin yafewa mutane 78 da suke tsare a gidan yari dake jihar.
Al-Makara ya bayar da wannan umarni ne a yayin da ya kai ziyarar musamman gidan yarin dake karamar hukumar Keffi, ta jihar Nasarawa.
Ya ce ya yi wannan hobbasa ne domin rage cinkuson da ake fama da shi a gidajen yarin kasar nan. “Yau, a madadin gwamnatin Jihar Nasarawa, ni Al-Makura na yafewa daurarru 78 wadanda laifusu bai taka kara ya karya ba.” In ji gwamnan.
Ya kara da cewa, wannan kadan kenan daga cikin irin kudurorin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari take yi na ganin ta rage cinkuso a gidajen wakafi.
Har ila yau, ya tabbtarwa da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida cewar, gwamnatinsa zata hada kai domin ganin an cimma nasara.
A nasa bangaren, Ministan Cikin Gida Abdulrahman Danbazau, ya yaba da wannan mataki, inda ya ce hakan zai taimaka kwarai wajen kawar da matsalar cinkuson masu laifi a gidan jarun. Ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki da su yi koyi da Gwamna Al-Makura domin ganin abubuwa sun tafi yadda ya kamata.
Wadanda dai suka samun wannan tagomashi ba wani babban laifi suka yi ba, yawancinsu bai fi matsalar bashi, harkallar kasuwanci da rigima ba.
Title :
Tanko Al-Makura Ya Yafewa Mutane 78 Dake Gidan Yari
Description : Gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji Umaru Tanko Al-Makura, ya bayar da umarnin yafewa mutane 78 da suke tsare a gidan yari dake jihar. Al-Makara ...
Rating :
5