A cewar Shugaba Buhari, duk wanda aka samu da hannu a badakalar kudaden sayen makamai na Dala bilyan 2.1, za a ingiza keyarsa zuwa kurkuku. Shugaban ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa.
A cewarsa, "Idan ba a manta ba, a lokacin yakin neman zabe mun ce Nijeriya tana fuskantar wasu manyan matsaloli guda uku wadanda babu wanda ya musunta hakan. Da farko akwai matsalar tsaro wadda ta mamaye Arewa maso Gabashin kasar nan, yayin da ake ta yi wa dukiyar mai zagon kasa a yankin Kudu".
"Abu na biyu, shi ne matsalar rashin aikin yi. Sai kuma na ukunsu, wato cin hanci da rashawa matsalar da ta yi wa kasar nan katutu. Idan kuwa ba mu hanzarta wajen dakile wadannan matsalolin ba, tabbas kasarmu za ta durkushe.
Wannan ne ma ya sa aka tsare wadanda suka saci kudin sayen makamai suka raba a tsakaninsu inda za a bukaci su dawo da kudaden ko kuma su fuskanci hukunci".
“Za mu yi amfani da bayanan da aka tattara wajen kafa hujja game da satar da suka tafka tare da kwace duka kadarorin da suka mallaka kana a ingiza su kurkuku", in ji Shugaban.
Title :
Su Dawo Da Kudaden Da Suka Sata Ko Kuma Su Fuskanci Hukunci - Buhari
Description : A cewar Shugaba Buhari, duk wanda aka samu da hannu a badakalar kudaden sayen makamai na Dala bilyan 2.1, za a ingiza keyarsa zuwa kurkuku....
Rating :
5