Yayin da al'amura ke ci gaba da dagulewa tsakanin sojan Najeriya da kuma 'yan Shi'a a cibiyarsu a Zaria, rahotanni na cewa, an kashe mukaddashin jagoran 'yan Shi'a a Najeriya Malam Muhammadu Turi.
Kafin dai kisan Malam Turi shi ne ke jagorantar 'yan Shi'a a Kano.
Rahotanni daga sassan Nigeria na cewa, 'yan Shi'a karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim El Zakzaky suna ci gaba da zanga-zanga a biranen Nigeria da dama da suka hada da Katsina, da Kano da kuma Potiskum.
Jiya ne dai aka soma wannan yamutsi, inda rundunar sojan Najeriya ta zargi 'yan Shi'a da kokarin halaka babban hafsansu Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai yayin wata ziyara a Zaria.
Amma 'yan Shi'a sun musanta zargin da sojan Najeriyar suka yi.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa tun kusan lokacin sallar Azahar aka fara rushe gidan na Sheikh Al-zazzaky, kuma duk da a yanzu kura ta dan lafa, akwai bayanai dake nuna cewa hayaki na tashi a gidan kuma tuni aka rushe shi.
Wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba sun ce an rushe Husainiyya, da masallaci da kuma Hedikwatar 'yan uwa musulmi, da dama daga cikin shugabannin su kuma ba a san inda suke ba.
Title :
Sojojin Najeriya Sun Kama El Zakzaky Bayan Sun Kashe Malam Turi
Description : Yayin da al'amura ke ci gaba da dagulewa tsakanin sojan Najeriya da kuma 'yan Shi'a a cibiyarsu a Zaria, rahotanni na cewa, an k...
Rating :
5