Wasu yan gudun hijira sun bayyana cewa sai da sukayi tsawon kwanaki suna tafiya kan hanya sannan suka isa sansanin yan gudun hijirar.
Maryamu Abubakar ta bayyana cewa a ranar Litinin 7 ga watan Disamba, sojojin Kamaru suka shiga wani kauye wanda yake kusa da mu, Banki, inda suka kashe mutane da yawa.
Abubakar ta bayyana cewa disjoin sun shigo kauyen inda suka kashe mutane kuma suka sace dabbobi da yawa. Tana cikin Mutane 643 wadanda suka isa sansanin yan gudun hijira dake Fangore a jihar Adamawa a ranar Litinin 7 ga watan Disamba 2015.
Wasu Sojoji da suka tantance su, sun bayyana cewa yan gudun hijirar sun taho me daga Gambaru zuwa Banki. Haka zalika gwamnan jihar Adamawa ya zargi kasar Kamaru da turo mutanen su a matsayin yan gudun hijira. Sannan ya bayyana cewa gwamnatin kasar ce ke turo dasu.
Kasar Kamaru ta musanta Haka inda ya bayyana cewa rana hada hannun ne da gwamnatin Najeriya domin a yaki Yan Boko Haram.
Ministan Mai na Najeriya ya bayyana cewa an kara samu Mai a Tabkin Chadi. Ya bayyana cewa Haka zaya Iya Kara kawo tashin hankali saboda a tsakanin kasashen Najeriya, Nija, Chadi da Kamaru.
Wata kungiya Mai rajin taimaka ma mutane wadda ke samun shugabanci daga David Miliband ta ziyarci jihar Borno Inda Ta bukaci kasashen dake nida da jihar su hada Kai.
A wannan makon ne kuma ministan tsaro Na Najeriya ya bayyana cewa sojojin Kamaru sun shigo Najeriya Inda suka kubutar da Mutane 900 da Boko Haram ke rige dasu.