Kungiyar Islamic Movement ta 'yan Shi'a ta ce, soja sun kashe mai ɗakin jagoransu, Malama Zeenat Ibraheem da ɗanta Ali Al Zakzaky.
Wata sanarwa dauke da sa sannun Malam Ibrahim Musa ta ce, yayin samamen da soja suka kai cibiyar 'yan Shi'a dake Gyallesu an kuma kashe jagoran kungiyar a Kano, Malam Muhammad Turi, da kuma kakakin kungiyar Ibrahim Usman da kuma likitansu Dokta Mustapha Sa'eed.
Sanarwar ta kuma ce, har yanzu ba a san inda jagoransu Sheik Ibrahim Al Zakzaky yake ba, kuma ba san halin da yake ciki ba.
Sun ce, an kashe mutane da dama a cibiyoyin da kungiyar ke ayukanta a Gyallesu, da GRA da kuma makabarta dake kan hanyar Jos.
'Yan Shi'a sun kuma sake musanta zargin sojan Najeriya cewa, sun yi yunkurin halaka shugabansu, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai.
Jiya ne dai sojan Najeriya suka zargi 'yan Shi'a da kokarin kisan babban hafsansu.
Ya zuwa yanzu dai soja ba su ce komai ba dangane da lamarin.
Title :
Soja Najeriya Sun Kashe Matan Al Zakzaky Zeenat
Description : K ungiyar Islamic Movement ta 'yan Shi'a ta ce, soja sun kashe mai ɗakin jagoransu, Malama Zeenat Ibraheem da ɗanta Ali Al Zakzaky. ...
Rating :
5