Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafi kudin da kasar za ta kashe a shekarar 2016, wanda suka kai naira tiriliyan 6.08. Kkasafin dai ana gabatar da shi ne gaban majalisar Dattaawa da ta Dokoki a yau Talata, 22 ga watan Disamba.
Buhari ya bai wa ‘yan Nijeriya hakuri bisan matsalar man fetur da yanzu haka take ci wa al’umma tuwo a kwarya, inda ya ce, hakan ta faru ne sakamakon gazawar gwamnatin baya wajen kyautata rayuwar ‘yan kasa. Ya kuma ce gwamnatinsa tana kokarin bin dukkan hanyoyin da suka dace domin tabbatar da ganin abubuwa sun daidaita.
Shugaba Buhari ya ce kaso 30 cikin 100 na kasafin zai fi mayar da hankali kan manyan ayyuka, inda aka daga darajar kudin daga naira bilyan 557 zuwa naira tiriliyan 1.8.
Ku biyo mu don jin karashen yadda kasafin kudi yake gudana.
Title :
Shugaba Buhari Ya Gabatar Da Kasafin Kudin Shekarar 2016 Gaban Majalisa
Description : Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafi kudin da kasar za ta kashe a shekarar 2016, wanda suka kai naira tiriliyan 6.08. Kkasafi...
Rating :
5