Yan Shi'a Sun Yi Laifi, Amma Hukuncin Da Sojoji Suka Yanke Ya Yi Tsanani, Inji Sheik Dahiru Bauchi
Shahararren Shehin Malamin nan Sheik Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa ba a samar da gwamnati cikin gwamnati don haka ya zama wajibi kowane dan kasa ya bi doka.
Shehin Malamin, wanda ya bayyana hakan a yayin hudubar Sallar Juma'a da ya gabatar a shekaranjiya, ya kuma kara da cewa duk da cewa mabiya Shi'a sun yi kuskure na tare hanya, bai kamata sojoji su dauki wannan mataki ba domin ya yi tsauri da yawa.
Shehin ya kara da cewa saboda muhimmancin dan Adam ne ya sa Allah ya samar da hukunci mai tsanani ga wanda ya kashe rai. Don haka tun farko kamata ya yi sojoji su yi amfani da barkonon tsohuwa da harsashin roba.
Shehin ya kuma yi kira ga al'ummar Nijeriya da su kasance masu bin doka da oda.
Title :
Sheikh Dahiru Usman Bauchi Yayi Magana Akan Rikicin Yan Shi'a
Description : Yan Shi'a Sun Yi Laifi, Amma Hukuncin Da Sojoji Suka Yanke Ya Yi Tsanani, Inji Sheik Dahiru Bauchi Shahararren Shehin Malamin nan Sheik...
Rating :
5