Shawarwari guda 60, ga masu gida domin samun zamantakewa mai inganci, da zama miji na gari.
1.ciyarwa gwargwadon iko.
2.tufatarwa daidai iko.
3.shayarwa.
4.kayan kwalliya.
5.kayan tsafta.
6.gurin kwana.
7.kula da lafiya.
8.hakkin saduwa.
9.ilmantarwa.
10.girmamawa.
11.mutuntawa.
12.tausasawa.
13.yabawa ga abinci ko kwalliya ko tsafta.
14.nuna damuwa da ita.
15.sakar mata fuska da murmushi.
16.gaya mata kalmomi masu dadi na yabo.
17.zama hira da tattaunawa da ita.
18.kiranta da suna mai dadi.
19.yawan yi mata kyautar ba zato ba tsammani.
20.fita unguwa ko taro ko ko tafiya da ita.
21.taimaka mata aikin gida ko dan kadan.
22.bata damar zabin abincin gida a wasu lokuta.
23.bata damar zabin tufafin da zata sauya.
24.mutunta iyayenta da danginta.
25.A bata hakuri idan anyi mata ba dai dai ba.
26.A yaba mata idan tayi daidai.
27. kada a zageta ko a muzantata a gaban yayanta.
28.banda duka.
29.banda zagi.
30.banda saurin fushi.
31.ka zama miji mai tsafta.
32.ka zama miji mai kula da goge baki.
33.miji mai kwalliya.
34.miji bamai almubazzaranci ba.
35.miji bamai mai kwauro ba.
36.miji bamai shan taba ba.
37.miji bamai mai shan giya ba.
38.miji bamai yawon dare ba.
39.miji bamai neman mata ba.
40 Kada ka zama miji mai hira da wasu mata a gaban iyalansa.
41.miji mai yawan fada.
42.kada ka zama miji mai kauracewa shimfidar iyali.
43.kada ka zama miji mai nuna rashin damuwa da halin da iyalansa suke ciki.
44.kada ka zama miji mai tsananin kishi.
45.kada ka zama miji mai yawan zagi.
46.ka nuna wa matarka cewa gamsu da yanayinta.
47.ka bata dama ta fadi raayinta.
48.kayi shawara da ita akan harkokin gida da wajen cikinta.
49.ka dinga sumbatar ta daga lokaci zuwa lokaci.
50.yin wanka tare a wasu lokuta.
51.rera mata waka da kirari.
52.yin wasa da guje-guje.
53.kada ya zama miji mai zargi.
54.kada miji ya zama mai mugunta.
55.kada miji ya zama mai kushe.
56.kada miji ya zama mai bakin ciki da abinda iyalansa suke dashi.
57.kada miji ya zama mai ragwanci.
58.mijin ya zama mai lafiya wajen biyan bukatar aure.
59.miji ya zama mai kaunar yayansa.
60.miji ya zama mai girmama kawaye da aminan matarsa
MU duba abubuwan nan 60 wanda muke yi na kirki mu kara ,wanda mukeyi na rashin kirki mu dena,
Allah ya bamu ikon rike iyalan mu da kirki da alkhairi.
Title :
Shawarwari Guda 60 Ga Masu Aure
Description : Shawarwari guda 60, ga masu gida domin samun zamantakewa mai inganci, da zama miji na gari. 1.ciyarwa gwargwadon iko. 2.tufatarwa daidai i...
Rating :
5