Yayin da a Nigeria ake ci gaba da jimamin tashin hankalin da ya faru tsakanin Sojoji da 'yan Shi'a a Najeriya, Mai martaba Sarkin Kano ya ce yakamata hukumomi a kasar su dauki matakin hana sake aukuwar irin rikicin a gaba.
A wajen wani taron addu'o'i na musanman da ya jagoranta, Sarki Muhammadu Sanusi na Biyu ya ce kamar yadda ya ke babu wata kungiyar addini da za ta mayar da kanta hukuma, suma jami'an tsaro bai kamata su rika bude wuta a kan kowane irin laifi ba.
Sarkin ya buka ci kungiyoyin addinai da su zamo masu da'a, da kaucewa tsokano fitina saboda ba a san karshenta ba, sannan gwamnati kuma ta rika jan hankalin jami'an tsaro da su rika hakuri kadan, saboda a takaita salwantar rayuka.
Baya ga matakin da sarkin Kano ke bukatar a dauka, wasu malaman addinin Musulunci na ganin matsalar tamkar gobara ce daga kogi, dan haka babban maganin ta shi ne addu'a, tun da dai Nigeria kasa ce da mabiya addinin musulunci da na kiristanci ke da yawa.
Daya daga cikin malaman addini da suka halarci taron addu'o'in, Ustaz Ya'u Husaini Dodo ya yi kira ga shugabanni a matakai da ban daban da su rika nada masu basu shawara kan sha'anin addini saboda kaucewa irin haka a gaba.
Su kuwa wasu masu fashin bakin al'amura na ganin wajibi ne a koma bin dokokin kasa, sannan kuma shugabanni su rika amfani da bayanai a duk lokacin da za su yi wani abu da zai iya hadawa da mu'amala da jama'a.
Majalisun dokokin tarayyar Najeriya ma sun kafa kwamitoci domin su binciki arangamar da ta auku tsakanin sojoji da 'yan kungiyar Shi'a a kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Majalisun sun yanke shawarar kafa kwamitocin ne a zaman da su kayi na sirri.
Title :
Sarkin Kano Yayi Magana Akan Rikicin Yan Shi'a
Description : Yayin da a Nigeria ake ci gaba da jimamin tashin hankalin da ya faru tsakanin Sojoji da 'yan Shi'a a Najeriya, Mai martaba Sarkin Ka...
Rating :
5