Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce ya yi shiru ne game da batun kisan da ake zargin sojojin kasar sun yi wa mabiya akidar shi'a domin kada hakan ya shafi bincike daban-daban da ake yi a kan rikicin.
Wannan kisa da ake zargin sojojin sun yi dai ya faru ne makonni biyu da suka wuce a garin Zaria da ke jihar Kaduna, bayan arangama da sojojin suka yi da mabiya mazhabar ta Shi'a.
Mai taimaka wa shugaban Najeriya a kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a cikin wata hira da BBC.
Ya furta hakan ne kan alhinin da shugaban ya bayyana game da ibtila'in gobarar tankar mai da ta faru a jihar Anambara.
Title :
Rikicin Yan Shi'a: Bincike Ne Ya Hana Ni Magana - Buhari
Description : Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce ya yi shiru ne game da batun kisan da ake zargin sojojin kasar sun yi wa mabiya akidar shi'a d...
Rating :
5