Wasu yam mata yan watanni 3 da haifuwa wadanda suke manne a kugu da kirji an samu raba su a wata asibiti dake Barara, Yankin Ambala a kasar Indiya.
Yan Matan Janar da Manat an haifi su a ranar 17 ga watan Oktoba in dauke fama da wannan matsala wadda turawa ke cema Omphalopagus. Amma anyi sa’a zuciya rasu da sauran Kayan ciki kowa nada bashi.
Dacta Ravi Kanojia, mataimakin farfesa na kananan yara da fida wanda ya jagoranci aikin yace: “Wanna wani abu ne wanda sau daya Likita yake ganin sa. Wannan shine karo na farko Wanda aka kawo Shi a nan PGIMER.
”Kafin a raba su, kowane su yana da nauyin 4kg 100g. Likitoci sunyi shawarar raba su da sauri. Likitoci 30 ne sukayi Masu aikin.”