Tsohon gwamnan jihar Rivers, Dakta Peter Odili a jiya Talata ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ce ta ba shi naira milyan dari domin tafiyar da harkokin jam'iyyar a yankunan Kudu maso Kudu a yayin zaben 2015.
Tsohon gwamnan ya musanta cewa ya karbi kudin ne daga wurin tsohon karamin ministan kudi, Ambasada Bashir Yuguda.
Ya kuma kara da cewa ba shi da wata harka da ya taba yi da tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki.
Odili, wanda ya bayyaana hakan a Abuja, ya kara da cewa milyan darin da aka ba shi, an ba shi ne a gidan tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Alhaji Adamu Mu'azu.
Rariya
Title :
PDP Ce Ta Ba Ni Milyan Dari Ba Bashir Yuguda Ba, Inji Peter Odili
Description : Tsohon gwamnan jihar Rivers, Dakta Peter Odili a jiya Talata ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ce ta ba shi naira milyan dari domin tafiyar ...
Rating :
5