''
Wani matsashi mai suna Fatai Sabitu mai shekaru 19, wanda ke sana'ar faci, wanda kuma ake zargin sa da kashe abokin sa mai suna Yusuf Sheu, ya bayyana cewa naushi daya kawai ya yi masa.
Fatai wanda dan asalin garin Abeokuta ne dake jihar Ogun, ya bayyana cewa bayan ya naushe abokin nasa mai shekaru 38 sun garzaya da shi asibitoci guda biyu kafin ya ce ga garin ku nan.
Kamar yadda majiyatmu ta rawaito, Fatai da Sheu sun samu sabani ne kan wata wayar sata. Mamacin, wanda dan asalin jihar Kwara ne, ya sayi wayar ne a wurin Fatai, wadda daga bisani aka gano cewa ta sata ce. Inda bayan asalin mai wayar ya karbe abar sa, sai mamacin ya bukaci a dawo masa da kudinsa wanda hakan ya kai su ga fada.
Title :
Naushi Daya Na Yi Wa Abokina Ya Mutu
Description : '' Wani matsashi mai suna Fatai Sabitu mai shekaru 19, wanda ke sana'ar faci, wanda kuma ake zargin sa da kashe abokin sa mai s...
Rating :
5