Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa (NAFDAC) reshen Kebbi, ta kone gurbatattun magunguna da kayan abinci na kimanin Naira miliyan 15.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin Shugaban Hukumar NAFDAC reshen Jihar Kebbi, Garba Abubakar Adamu a lokacin kone magungunan da hukumar ta yi a cikin dajin Kola da ke karamar Hukumar Birnin Kebbi.
Garba Abubakar Adamu ya ci gaba da cewa wadannan magungunna da kayan abinci an kwace su ne a hannun ’yan kasuwa masu yawo a kan tituna da kuma wadanda ke da shaguna. Ya ce an kone magungunan ne saboda yawancinsu sun gama aiki wasu kuma ba su da rajista da hukumar ta NAFDAC.
Shugaban hukumar ya kara da cewa, duk kokarin da hukumar ke yi a kullum wajen yaki da masu wannan muguwar sana’a abin sai gaba-gaba yake yi, saboda haka ya nemi kananan hukumomin jihar su hada hannu da Hukumar NAFDAC da zimmar samar da kwakkwarar hanyar shawo kan wannan babban lamari kasancewar kullum masu wannan sana’a yawaita suke yi.
Ya ce hukumarsu tare da hadin gwiwar jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya da masarautan jihar da ’yan jarida sun dukufa wajen tsince ire-ire wadannan magunguna da nau’in kayan abinci masu cutarwa.
A karshe ya nemi jama’a su rika kula a yayin da suka je sayen magunguna da nufin kauce wa sayen gurbatattun da kuma wadanda wa’adin aikinsu ya kare don kauce wa kamuwa da cututtuka.
Title :
NAFDAC ta kone magununan Naira miliyan 15 a Kebbi
Description : Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa (NAFDAC) reshen Kebbi, ta kone gurbatattun magunguna da kayan abinci na kimanin Naira ...
Rating :
5