Fitaccen Malamin Addinin nan dake zama a garin Kaduna, Sheik Dakta Ahmad Abubakar Gumi a jiya Talata ya yi jawabi kan rikicin da ya auku tsakanin sojoji da 'yan shi'a, inda ya ce tun farko dama ya sha jan kunnen Sheik Ibrahim Zakzaky kan tare babbar hanya a yayin da suke taro.
Ya ce shugaban 'yan Shi'an da mabiyansa sun kai kusan shekaru 40 suna cin karen su ba babbaka a yankunan Arewa.
Sheik Gumi ya bayyanawa manema labarai a jiya a jihar Kaduna cewa 'yan Shi'an suna horar da sojoji na kansu, inda ya ce suna gwamnati cikin gwamnati.
Title :
Na Sha Jan Kunnen Sheik Zakzaky Kan Tare Hanya A Yayin Taro- Sheik Gumi
Description : Fitaccen Malamin Addinin nan dake zama a garin Kaduna, Sheik Dakta Ahmad Abubakar Gumi a jiya Talata ya yi jawabi kan rikicin da ya auku ts...
Rating :
5