DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA
Sama da mutane 30 ne suka rasa rayukansu a yayin wani munmunan hatsarin Kwale-Kwale da ya afku a kogin Gilmu dake kauyen Gaja-gaja na yankin karamar hukumar Kubau ta jihar Kaduna, a ranar Talatar da ta gabata.
Da yake bayyana yadda al'amarin ya faru, Sarkin rafi na Gaja-gaja, Malam Bala Gaja-gaja, ya ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 12 na daren ranar Talata, sakamakon lodi fiye da kima da matukin kwale-kwalen ya yi, inda a ka'ida ya kamata a ce kwale-kwalen ya dauki mutane 21 ne, da kaya masu nauyin kilo 20, amma a maimakon haka sai aka dankara mutane 45 cikin shi da wasu kaya masu nauyi kilo 200, wanda shine ya sabbaba nutsewar kwale kwalen, amma cikin yardar Allah sun yi nasarar ceto mutum goma, yayin da 35 suka rasu.
Malam Muhammadu Gaja gaja shine dagacin kauyen, ya bayyana cewar musamman yake halartar inda masu aikin kwale kwalen suke, yana yi musu hudubar daukar fasinja fiye da kima, amma abin takaici yawancinsu ba su jin hudubar, suna yin gaban kansu.
Za ku iya tura mana naku labarai ta shafin mu na Facebook
Title :
Mutane 35 Sun Rasa Ransu A Wani Hadarin Kwale-kwale A Jihar Kaduna
Description : DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA Sama da mutane 30 ne suka rasa rayukansu a yayin wani munmunan hatsarin Kwale-Kwale da ya afku a kogin Gilmu da...
Rating :
5