Hadin kai yana daya daga cikin abinda yake ciwa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya, musamman ma ta bangaren fahimta da mutunta addinin juna. Wanda masu tsokaci ke ganin hakan ne ma yake haifar da yawan fitintinun da ake samu tsakanin addinan kasar musamman Kirista da Musulmi.
Jihar Kaduna a Najeriya na daya daga cikin jihohin Najeriya da suka sha fama da wannan matsala ta dauki ba dadin maganar bambancin addini wanda hakan yayi sanadiyyar salwantar mutane da dama. Ga dukkan alamu wannan yanayi yana shudewa a hankali sakamakon abinda bahaushe ke cewa kan mage yaw aye.
Wasu masu fashin baki ma gani suke yi ‘yan siyasa na taka mummunar rawar gani sosai a maganar fadan addini don cimma manufofin siyasa bayan sun yi makadin na gal-gal, wato sun had aba tare da raba fadan ba.
Gayyatar Kiristoci zuwa yin buda baki da azumin watan Ramadan da bukukuwan Sallah, ko kuma gayyatar Musulmi halartar bikin Kirisimeti ya fara zama dabi’ar wasu shugabannin addinai a Kaduna irinsu Fasto Yohanna Buru, wanda ya hada liyafar da ya gayyaci musulmi taya su ci da sha a bikin Kirisimeti.
Bikin da ya zo kwana daya tsakaninsa da Maulidin Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata a gareshi da aka yi ranar Alhamis, aka kuma yi Kirisimeti a jiya Juma’a, inda Kiristocin ke tunawa da Annabi Isa aminci ya tabbata a gareshi. Ga rahoton wakilin Muryar Amurka Nasiru Yakubu Birnin Yero.
VOA Hausa
Title :
Musulmai Da Kiristoci Sun Taya Juna Murnar Maulidi Da Kirisimeti A Jihar Kaduna
Description : Hadin kai yana daya daga cikin abinda yake ciwa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya, musamman ma ta bangaren fahimta da mutunta addinin juna. Wanda ...
Rating :
5