Sakamakon rasuwar Sarkin Keffi, Alhaji Mahammadu Chindo Yamusa II a ranar 4 ga watan nan, babban dansa, Dakta Shehu Usman Yamusa II ya maye gurbin mahaifinsa, bayan ya yi nasara samun kuri'u biyar cikin bakwai a zaben da aka yi.
A jawabin da sakataren gwamnatin jihar Nassarawa, Ambasada Umaru Azores Suleiman ya yi, ya bayyana cewa sakamakon nasarar kammala zabe da aka yi a yau domin fitar da sabon Sarki, gwamna Umaru Tanko Al-Makura bisa taimakon mahukuntan Masarautar, ya nada Dakta Shehu Usman Yamusa II a matsayin sabon Sarikin Keffi.
Sabon Sarkin Keffi, Dakta Shehu Usman Yamusu II, an haife shi a ranar 4 ga Nuwamba, 1966. Ya halarci jami'ar Usman Danfodio dake jihar Sokoto da jami'ar Dundee a kasar Scotland da kuma jami'ar Musulunci da ke kasar Malesiya.
Kafin ya zama Sarki, lakcara ne a sashen shari'a a jami'ar Nassarawa dake garin Keffi.
*Hoton Marigayi Sarkin Keffi, Chindo Yamusa II
Title :
Masarautar Keffi Ta Yi Sabon Sarki
Description : Sakamakon rasuwar Sarkin Keffi, Alhaji Mahammadu Chindo Yamusa II a ranar 4 ga watan nan, babban dansa, Dakta Shehu Usman Yamusa II ya maye ...
Rating :
5