An tabbatarwa jama'ar tarayyar Nijeriya cewar, zasu wadatu da albarkatun man Fetur har ya zarce bukatunsu, inda zai zamana man fetur zai kasance tamkar ruwan sha ga kowa, a shekara mai zuwa ta 2016.
Ministan kasa a ma'aikatar albarkatun man fetur Dr Emmanuel Ibe Kachukwu, ya bada wannan tabbacin, lokacin da yake jawabi gaban manema labarai, a yayin wata ziyara daya kawo matatar man fetur dake Kaduna a ranar Lahadin nan.
Ministan ya kara da cewar, shugaban kasa Muhammadu Buhari, yayi dukkanin mai yiyuwa wajen magance manyan matsalolin da sukayiwa manyan matatun man fetur uku da ake dasu a kasarnan tarnaki, wato matatar mai ta kaduna, data Fatakwal da kuma matatar mai dake birnin Ikko, inda zai zamana cewar zasu rinka tace Litar Mai har Miliyan 10 a rana guda.
Dr Ibe Kachukwu ya cigaba da cewar, batun janye tallafi ko tallafin mai ba shine abin maganaba, babban abin magana shine yaya za'ayi mai ya wadatu jama'a inda kowa a kasa zai gamsu da cewar an shawo matsalar man Fetur, wanda kuma shine matakin da shugaban kasa ya dauka.
Ministan ya kuma tabbatar da cewar babu wata maganar sayar da matatun man fetur a kasar nan, saidai abinda ake batu akai shine gwamnati zata sanya 'yan kasuwa a cikin tsarin inda zasu zuba jari a ciki, domin amfanar 'yan kasa gaba daya.
Title :
Man Fetur Zai Wadaci Jama'ar Kasa Har Ya Zarce Bukatunsu, Inji Ministan Man Fetur
Description : An tabbatarwa jama'ar tarayyar Nijeriya cewar, zasu wadatu da albarkatun man Fetur har ya zarce bukatunsu, inda zai zamana man fetur zai...
Rating :
5