Majalisar Matasan Musulmai ta Nijeriya ta kammala taron koli a Abuja babban birnin tarayya, inda ta kudiri aniyar kawar da rigingimun da suka addabi kasar.
Taron ya tattaro matasan musulmai daga sassa daban daban na jihohi 19 dake arewa.
Taron ya duba kalubalen da kasar ke fuskanta da kuma bullo da sabbin dabarun magance matsalolin.
Injiniya Alhed Yakubu Jimba mataimakin shugaban kungiyar ta kasa kuma mai kula da jihohin arewa yace duk rayuwar da ba'a sama mata matsaya ba to an maida ita kayan aikin Shaidan. Akwai bukatar iyaye su yiwa 'ya'yansu tarbiya ta kwarai. Dole ne kuma malaman addini su tashi su yi fada, wato su dinga tsawatawa. Sarakuna ma su tashi su yi fada. Gwamnati ma ta samarda yanayi da zai bada damar yin aiki. A koyawa matasa sana'o'i.
Mai masaukin baki Sani Suleiman Maigoro kuma sakataren kungiyar na jihohin Arewa ya ce taron ba na shan shayi ba ne.
Yace hadin kai shi ne na farko. Ya kuma kara da cewa suna da matsala dukansu kuma dukansu suna da rawar da zasu taka. Matukan ba'a sa matasa bisa sahihin addini ba to akwai matsala. Saboda haka malamai su mayar da hankali wajen samarda ilimi ingantace da zai dora matasa akan fahimtar addini.
Title :
Majalisar Matasan Musulman Nijeriya Ta Lashi Takobin Dakile Rigingimu
Description : Majalisar Matasan Musulmai ta Nijeriya ta kammala taron koli a Abuja babban birnin tarayya, inda ta kudiri aniyar kawar da rigingimun da suk...
Rating :
5