Majalisar Dattawa a Najeriya zata gudanar da bincike akan rikicin daya faru a Zariya inda aka kashe mutane da dama.
Shugaban kwamitin kula na yan sanda, Abu Ibrahim, ne ya bayyana haka inda ya bayyana cewa a yau za’a fara gudanar da binciken.
Bayan amrikicin ya auku, majalisar Dattawa ta kafa kwamitin wucin gadi na mutane 16 domin gudanar da bincike akan lamarin.
Shugaban kwamitin tsaro, Ahman Lawan ya bayyana cewa yanzu majalisa na hutu ne, amma sun dawo domin gudanar da wannan binciken.
Sannan ya bayyana cewa basu san ko za’a zo da Ibrahim El-Zakzaky ba.