Assalamu alaikum!
Malam ina hadaka da girman Allah, ka taimaka mani da maganin ciwon sanyi (gonoria). nasha maganin bature amma sai farin ruwa, kaikayin matsematsi dana jiki, gamida kananan kuraje a gabobina. Sai ya tafi sai ya dawo, sannan da ramewa kuma duk da ina cin abinci. Allah ya taimake ka yanda kake taimako.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Ka nemi Hulba ka rika dafawa tare da Kwayoyin tafarnuwa kana sha kullum da safe.
Sannan ka nemi 'Ya'yan cikin BADO, Ka dakasu sosai. Sannan ka samu ganyen RAIHAN shima ka dakashi sosai. Ka samu ganyen Duman Rafi shima ka dakashi sosai.
Kowannensu ka debi cokali Uku uku, Citta da kanumfari ma haka.. Ka hada da Garin Tafarnuwa cokali Uku, Garin Habbatus sauda shima Cokali uku, Garin Habbur Rashad shima haka.
Gaba dayansu sai ka juyesu acikin Zuma, Ka gaurayasu ka rika shan Cokali uku safe da rana da yamma.
In sha Allahu zaka samu Waraka acikin Qankanin lokaci da yardar Allah. Amma har matarka ma Zata sha. Kuma zaku dena Kusantar Juna alokacin da kuke shan maganin.
Shi kuma Wannan kaikayin, ka nemi MUMTAZ na Zauren Fiqhu ka rika shafawa acikin Matse-matsin naka. In sha Allahu zaka samu waraka.
Allah yasa adace.
WALLAHU A'ALAM.
Title :
Maganin Ciwon Sanyi
Description : Assalamu alaikum! Malam ina hadaka da girman Allah, ka taimaka mani da maganin ciwon sanyi (gonoria). nasha maganin bature amma sai farin r...
Rating :
5