*Wasu Yara 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Halaka Kansu Da Wasu Mutane Tara
Kwamitin bincike a garin Maiduguri ya wanke wani mai suna Abubakar Sadik wanda aka kama a kwanakin baya a matsayin daya daga cikin 'yan Boko Haram guda dari da sojoji suke nema ruwa a jallo.
Idan za a iya tunawa, Abubakar wanda yake aikin gadi a gidan Muhammad Daggash dake garin Maiduguri, an kama shi ne da nufin cewa shine lamba na 28 a hotunan 'yan Boko Haram din da sojoji ke nema ruwa a jallo.
Amma bayan gudanar da bincike kwamitin ya gano cewa an yi kuskure ne wajen sanya hotonsa. Inda tuni aka sake shi ya koma ga iyalansa. Sannan kuma an nesanta iyalan gidan Dagash din da al'amuran ta'addanci a jihar Borno.
A gefe daya kuma, a yammacin jiya wasu yara 'yan kunan bakin wake su uku da shekarun su bai wuci goma zuwa sha biyar ba sun halaka kansu tare da wasu mutane tara, inda 24 suka samu rauni. Lamarin ya auku ne a garin Banisheik a jihar Borno.
Title :
Kwamitin Bincike Ya Wanke Wani Da Aka Sanya Hotonsa Cikin Mutane Dari Da Sojoji Ke Nema
Description : *Wasu Yara 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Halaka Kansu Da Wasu Mutane Tara Kwamitin bincike a garin Maiduguri ya wanke wani mai suna Abubak...
Rating :
5