Kungiyar kare hakkin Musulmi a Nigeria, MURIC ta yi watsi da batun yuwuwar gwamnatin kasar na haramta saka hijabi idan ba a samu saukin hare-haren kunar bakin wake ba.
Buhari zai dauki matakin ne domin kare jama'a daga fuskantar hare-haren 'yan kunar bakin wake.
Sanarwa da Farfesa Ishaq Akintola ya fitar a madadin kungiyar, ta ce matakin tamkar fakewa da guzuma ne a harbi karsana.
Kungiyar ta fitar da sanarwar ce domin mayar da martani ga kalaman shugaba Muhammadu Buhari a hirarsa da 'yan jarida, na cewar mai yiwuwa gwamnatinsa ta haramta sanya hijabi idan 'yan Boko Haram suka ci gaba da yin amfani da mata domin kai hare-haren kunar bakin-wake a arewa maso gabashin kasar.
Hijabi dai ya kasance suturar matan aure da 'yan mata Musulmi masu daman gaske a Najeriya, musamman ma a arewacin kasar.
Sai dai a baya-bayan nan hare-haren kunar bakin-wake da 'yan mata masu sanye da hijabin ke yi sun fara sanya shakku a zukatan mutane dangane da kimar macen da take sanye da irin wannan tufafi.
A lokacin taron ECOWAS da aka yi a Abuja a makonnin da suka wuce, kungiyar ta yi barazanar haramta saka nikabi domin magance ayyukan 'yan ta'adda
Title :
Kungiyar Kare Hakkin Musulmi Ta Kasa Ta Mayarwa Da Buhari Martani Kan Yunkurin Haramta Sanya Hijabi
Description : Kungiyar kare hakkin Musulmi a Nigeria, MURIC ta yi watsi da batun yuwuwar gwamnatin kasar na haramta saka hijabi idan ba a samu saukin har...
Rating :
5