Jam'iyyar adawa ta PDP ta yi kira ga al'ummar Nijeriya da su yi amfani da damar zagayowar watan Maulidi da na Kiristimeti domin yin addu'ar samun hadin kan al'mmar kasar da samun ingantaccen tsaro da kuma fatan fita daga matsalar tattalin arzikin da kasar ke ciki.
PDP ta ce yin addu'a ta musamman din ya zama wajibi, musamman a daidai lokacin da kasar ke cikin mayuwacin hali na tabarbarewar tattalin arzikin kasa, wanda ya kara munana tun daga lokacin da APC ta karbi gwamnati watanni bakwai da suka gabata.
Jam'iyyar ta bayyana hakan ne a yau Alhamis, ta bakin sakatarenta na kasa, Olisa Metuh, inda ta ce maimakon sukar gwamnatin Buhari, akwai bukatar al'ummar Nijeriya su ajiye bambancin addini ko na siyasa a gefe su hade kansu domin yin amfani da wadannan bukukuwa masu muhimmanci wajen yin addu'ar kawo karshen matsalolin da suka addabi kasar.
Title :
Ku Daina Sukar Gwamnatin Buhari, Sakon Jam'iyyar PDP Ga Al'ummar Nijeriya
Description : Jam'iyyar adawa ta PDP ta yi kira ga al'ummar Nijeriya da su yi amfani da damar zagayowar watan Maulidi da na Kiristimeti domin yin...
Rating :
5