Bayan da tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Kanal Sambo Dasuki ya gabata gaban kotu jiya Litinin kan
zargin yin sama da fadi da makudan kudaden sayen makamai, bincike ya nuna cewa lauyan dake kare shi zai koma kotun don duba yiwuwar samar masa beli, duk da cewa za a ci gaba da shari'ar.
Saidai hukumar EFCC ta bayyana kwararan
hujjoji da za su sa a hanashi beli domin zargin da ake yi masa da yin almundahana da
sama da miliyan dari shida da kuma sama da
dala biliyan biyu.
Haka su ma sauran da ake tuhumar su tare da laifuka makamantan haka, irin su tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa da dansa Sagir da tsohon karamin ministan kudi da sauransu ana sa ran duba yiwuwar bada belin nasu.
Title :
Kotu Za Ta Duba Yiwuwar Bada Belin Su Dasuki A Ranar Juma'a Mai Zuwa
Description : Bayan da tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Kanal Sambo Dasuki ya gabata gaban kotu jiya Litinin kan zargin yin sama...
Rating :
5