Ladi ta damu kwarai da yanda Mama ke d'aure mata fuska,ta rasa ta ina zata soma bata hakuri. Har magana tayi kwana biyu amma har lokacin Mama bata sake mata ba. Koda an tashesu daga makaranta,idan taje shagon ba bata wani sakar mata fuska ko kad'an. Dayake tun soma zuwa makarantar Ladi,Mama ta nemi mataimakiya anan unguwarsu,Saratu. Itama bazawara ce mai yara har uku mijinta ya rasu. Tana samu kwarai ta karkashin Mama,daman rayuwace ta wahala sai dakyar take samun abunda zataci da yaranta bayan tayi wankau.
Rannan dai Mama na zaune akan darduma bayan ta idar da sallah,Ladi ta matsa gefenta ta zauna. Mama ko kallonta batayi ba ta k'ara tamke fuskarta.
"Mama don Allah ki yafemin ki bar fushi dani. Nayi maki kuskure babba amma in sha Allahu bazan k'ara ba. Nayi matukar yin nadama."
Mama ta tabe baki
"Yo kada kiyi ma Ladi,ai yin naki ma na dole ne. Don baki samu yanda kikaso ba. Ba'a yiwa namiji rawar kafa haka. Kije kiyi tayi na daina sanya baki."
Hawaye suka zubowa Ladi,ta kwantar da kanta akan cinyar Mamanta
"Nayi nadama,nasan na aikata ba daidai ba. Bani da mai rarrashina a duniya sai ke,domin Allah ki yafemin. Bansan yaushe na fara son yaya jafar ba,amma nayi maki alkawari daga yau zan yakiceshi a zuciyata. Ki tayani addu'a."
Mama cike da tausayawa ta shafi gashinta
"Zan tayaki,ki manta dashi. Allah Ya yaye maki sonshi idan ba alheri. Kamar yanda na sha gayamaki ne Matar mutum kabarinsa. Yanda dole sai ya shiga kabarinsa haka dole sai ya aureta. Mu dage da addu'a."
Murmushi Ladi tayi,taji dadin maganar Maman nata. Hawaye suka k'ara gangaro mata,tayi imanin cire Jafar a ranta ba k'aramin aiki bane. So kenan,ba wuya ya shiga saidai cireshi aiki ja ne.
********
Anti Habiba ta kurawa Jafar idotana mamakin yanda ya rame. Shi kuwa abincin data sanya aka kawo mishi kawai take narka. Rabonsa da abincin kirki tun ranar daya baro unguwarsu Ladi. Saida yaci ya k'oshi sannan ya d'ago yana shan ruwa ya dubi yayarsa. Murmushinyak'e tayi mishi kafin tace
"Sannu,ka zama gwauro na kwanaki gashi har ka rame."
Jafar shima murmushin yayi yana shafa wuyansa
"Ni kaina ina mamakin ramata antina,mai yiwuwa harda dan rashin lafiyar da nayi a kwanakin nan ne."
Ta jinjina kanta
"Hakane,Allah Yasa mu dace."
"Amin antina."
Ya d'anyi shiru kafin ya d'ago cike da damuwa ya dubeta
"Anti ga wata matsala fa ta bullo min."
Anti ta fiddo ido cikin fad'uwar gaba tace
"Allahu,meke faruwa kuma Kakana?"
Jafar ya yamutsa fuska kad'an yace
"Hajiyar Siyama tayi kirana jiya,ta bud'emin wuta akan dole sai na kawo kud'i an dinkawa Siyama kayan fita yawon arba'in. A cewarta wai tunda ba suturar arziki nake yiwa Siyamar ba ai ya dace nasan abunda ya kamata nayi mata kafin ranar ko don gudun abunda munafukai zasu ce cikin danginsu."
Anti habiba batasan sadda ta runtumo ashariya ba kafin tayi istigfari daga baya
"Har sun sanyani ashariya,wai me mutanen nan suka daukemu ne? Na k'ara gaskata cewa Hajiya Maimuna batasan abunda ya kamata ba. Wannan wane irin sabon tsirfa ne! Toh wallahi Kakana idan na samu labarin ka bayar da ko tsinke sai ranka yayi mugun b'aci. Wannan zubda girma da mutuncin da me yayi kama? Hajiya Maimuna tana da ilimi amma batasan tayi aiki dashi ba? Toh barni dasu, zanje har gidan na samu Siyama."
Ta inda anti habiba take shiga batanan take fita ba. Kana ganinta kasan ta dauki zafi sosai. Jafar dai shiru yayi don ma bai gayamata gorin arzikin da Hajiyar ke yi mishi ba ai da baisan yanda antin zatayi ba. A karshe ta k'ara gargadinshi akan kada ma ya sanarwa Hajja domin tana iya cewa ya basu don a zauna lafiya.
Da wannan sukayi sallama akan Antin zataje gidan da kanta.
"Assalamu alaikum."
Ta amsa gami da waigowa don ganin mai sallamar,nan da nan ta chanja fuska,Anti Habiba ta lura da ita saidai ta share ta k'arasa tana mai zama akan kujera.
"Hajiya ina wuni,ya yammaci."
Cikin halin ko'in kula Hajiya ta amsa a takaice
"Lafiya."
Kafin anti habiba tayi wata magana,Siyama ta fito sanye da riga doguwa na material. Kitson nan tun na suna shine har yanzu a kan nata bata tsefeshi ba. Ganin Anti Habiba saida gabanta ya fad'i,ta daure cikin sakin fuska😀 ta k'arasa
"Anti sannu da zuwa."
"Yauwa Siyama,sannunkikema ya jego? Ina d'an namu?"
"Bai jima da kwanciya ba."
Anti habiba ta gyada kanta
"Ki daina kwantar dashi,da zarar yamma tayi anfison a goya yaro ko a rikeshi a hannu. Allah Ya kiyaye."
"Toh anti,bari na kawomaki ruwa."
Bata hanata ba,bayan fitarta ta dubi Hajiya tana murmushi
"Hajiya magana nazo muyi."
Hajiya wacce har lokacin bata saki fuskarta ba ta dubeta kad'an sannan ta dauke kanta tare da rage sautin TV da take kallo.
Wannan ya nunawa Anti cewar tana sauraronta.
"Naji wani sabon al'amari ne daga bakin Jafar akan sai yayiwa ankon fita yawon arba'in wanda ko kusa ni ban tabajin inda akayi wannan ba ko a al'adance. Toh kasancewar kinsan shirme na kannenmu na yara mata yanzu naga gwara nazo da kaina naji koda saninki ne Siyama ta tafka wannan kuruciyar ko kuwa dai ta rufeki ne?"
Tunda tayi kiran sunan Jafar a maganar,Hajiya ta soma jifanta da wani gira,tana mai k'ara hade gira. Saida takai aya sannan Hajiya ta soma magana cike da gadara.
"Tushen zancen daga uwar Siyama ta fito ba Siyamar ba. Kayane Jafar zai yiwa Siyama domin duk cikin kayanta daga na lefe zuwa na suna da yayi banga wata tsiyar da Siyama zata sanya ta shiga zuri'ar Abba Tukur da sunan yawon zumuncin arba'in ba Habiba. Don haka idan ma wai turoki yayi don ya nemi alfarmar a janye wannan bamai yiwuwa bane,d'iyata bata tab'a sanya k'aramar atamfa ko leshi ta shiga taron mutane ba saida taje gidan Jafar. Wannan abun kunyar bazan k'ara bari a maimaita mini shi ba ni Maimuna. Gwara ki tashi kije ki ja mishi kunne ya cika umarnina ya sauke hakkin dake rataye a wuyanshi."
Tana maganar ne hankali kwance har ma tana chanje chanjan channels,tuni Siyama ta dawo daga kawo ruwa ta dire tana gefe jiki ba kwari ganin yanda anti habiba ta gama fusata. Wannan yasa Hajiya tana kaiwa aya,ta cafe
"Haba Hajiya,wannan irin magana bai dace yana fitowa daga bakinki ba. Inace da Jafar da Siyama duk d'aya ne a wajenki..."
Da sauri Hajiya ta dakatar da ita
"A'a a'a,menene had'in kashi da fura?Gyara maganarki Habiba. Kada ki manta Siyama d'iyar cikina ce."
"Naji wannan,toh amma ku sani,Jafar yayi iyakar kokarinsa akan d'iyarki tun kafin zuwan wannan rana. Kada ma kiji da wai,tun suna saurayi da budurwa babu kalar hidimar da Jafar baya yiwa Siyama gatanan zaune ki tambayeta.,abar wannan batun ma,ke Siyama kiyi rantsuwa da Allah Jafar bai siya maki suturu masu tsada daidai karfin aljihunsa? Wane irin kulawa kike baiwa suturinki? Toh hajiya kafin ki soma zagin Jafar ki soma zagin Siyama,domin ni tunda nake a rayuwa ban taba cin karo da wacce bata damu da kula da komai na rayuwarta ba sai Siyama. Alhamdulillah,Jafar bashi da arzikin siyan manya sufofi da shaddodi a haka Jafar bai fasa yi mata siyayyan kaya na adon fuska da jiki. Ko cikin kala ukun da Jafar yayi na suna,Hajiya saidai ki take gaskiya amma a matsayinki na wacce ta saba d'ora super da sauran tsadaddun yaduna da sarkoki kinsan Jafar ya sayi abunda yafi karfin aljihunsa hakanan rago har biyu ya samarwa d'ansa na sunansa. Idan duka wadannan basuyi maku ba sai ki k'ara sanya diyarki a d'aki ki bata ilimi akan zamantakewar aure,babban abunda ke kod'ar da suturunta bai wuce kasacewarta muguwar k'azama ba! Amma nayi rantsuwa ba zanyi kaffara ba ko tsinke na Jafar ba zaku samu ba idan yaso tayi yawo tsirara!"
Daga haka anti ta mike tayi hanyar fita,Hajiya ta kurma ihu
"Nashiga uku ni Maimuna! Habiba ashe ke yar iska ce bansani ba? Ni kike gayawa bakaken maganganu? Shegiya wacce batayi gadon arziki ba. Wallahi har gidan uwartaki zan shiga,daman haka kike?"
Tuni Anti habiba tayi waje,daman saida ta soma shiga gidansu ta gama yininta sannan ta shiga ko hajja batasan kudurinta kenan ba. Titi kawai ta nufa ta hau mota ta tafi.
Hajiya sai ashar takeyi,Siyama banda kuka babu abunda takeyi. A fusace ta kai mata bugu
"Yar iskar yarinya! Duk kece kika janyomin wannan bakin cikin! Amma wallahi kowa yaci tuwo dani miya yasha(hope hakane)!"
A fusace tayi dakinta sai gata ta fito da mayafi akanta tayi hanyar waje,ganin haka da sauri Siyama ta rikota tana kuka
"Don Allah Hajiya kada kije gidan,abar maganar kayan."
A fusace ta wanke mata fuska da mari ta tureta
"Allah Ya sauwake da hali irin naki Siyama! Banza shashashar wofi kawai wacce batasan a tab'a uwarta ba taji zafi. Toh na rantse yau sai na rama akan Fa'iza.!!!"
Daga haka tayi waje tabar Siyama anan tana kuka,can kuma ta jiyo kukan Faruk ta mike ta nufi wajensa....
Wai akwai rigima..kenan..!