Duk da kallon da yake binta dashi na tsantsar mamaki,wannan bai hana Ladi k'ara nufoshi ba dauke da murmushinta wanda ya sauya kama zuwa na mai nishin kashi.
"Assalamu alaika yaya j."
Tayi namijin kokari wajen yin furucin sallama gareshi,yayindaJafar yayi mutuwar tsaye ba tare daya iya amsawa ba. Ya d'ago yatsansa ya nunata
"Ladi!! Kada dai ace kece Hadiyya?!"
zuciyarta na fat fat,ta daure ta runtse idonta
"Kayi hakuri yaya j,kwarai kuwa nice Hadiyya."
"No!!! I cnt believe it! Ladi meke faruwa ne?"
Tuni kwallah ta cika idonta,ta waiga taga mutanen wurin harkokin gabansu kawai sukeyi. Ta fiddo wayarta ta bud'o sak'onnin da suka dunga musayarsu ga juna. Ta mik'a masa cikin rawar murya tata mik'a mishi
"Wannan kad'ai ya isheni shaida yaya j. Na rantse da Allah zuciyata bata nufinka da sharri."
Ya kalleta kafin ya sanya hannu ya karb'i wayar,ransa yayi tsananin b'aci. Jikinsa ya hau rawa,ya kauda kansa ya mik'a mata wayarta. Yayi shiru zuciyarsa na k'una,kafin ya d'ago jajayen idanunsa wadanda bacin rai ya rina ya dubeta,tuni Ladi ta soma ruwan hawaye
"Nasan ni hakika mai laifi ce yaya j,nasan nayi abunda addininmu ya haramta. Ina rokon gafararka,kayi uzuri ga zuciyar data riga ta gama tsumuwa da soyayyarka. Wallahi yaya j...."
"Dakata!! Banason jin komai daga gareki. Tsakanina dake akwai Allah! Kin cuceni Ladi,kin cuceni!"
Daga haka ya hau mashin d'insa,da sauri ta dafe kan mashin d'in har tana had'awa da hannuwansa kafin ta kautar da hannuwanta da sauri. Durkusawa tayi gwuiwoyinta a k'asa tana kuka sosai gaba d'aya 'yar kwalliyar tarbar mijin kazamatuya goge
"Kada kayimin haka yaya j,bakasan wahalar dana sha akan kaunarka ba. Yaya j bakasan yanda zuciya da gangar jikina suke azabtuwa a dalilin kaunarka ba. Yaya j rashinka a rayuwata ba k'aramin tashin hankali bane a gareni. Idan da gaske kake kanason Deeya,me zai sanyaka ka guji Ladi? Yaya j me zanyi ka yafemin laifina? Ko menene na shirya yinsa amma domin Allah kada ka barni."
Yayi tsai yana dubanta,har ta soma tunanin ya hakura saidai taji ya tayar da mashin d'insa da saurinta ta mike tsaye tana kokarin tsayar dashi. Ya girgiza kanshi
"Kin yaudareni Ladi! Bazan taba cigaba da mu amala dake ba...!"
Daga haka ya ja mashin d'insa inda yabar Ladi cikin tsananin nadama. Ta yarda SO BABBAR CUTA ne!!tom mudai du Abdool allah yaymana maganin namu chutan..!
Da gudu gudu ta shige gidansu ta fad'a jikin mamanta tana kuka. Cikin tsananin gigitaMama ta d'ago fuskarta tana salati
"Yau ni Binta na shiga uku! Ke menene? Meya faru?"
Sai kuma ta mike da saurinta ta fito waje tana lek'e amma idonta bai gane mata kowa tsaye a kofar gidan nasu ba. Ta dawo da sauri tana jijjiga kafadar Ladi
"Ki tashi ki gayamin me yayi maki? Wanene?"
Ladi ganin yanda Mama ta rud'e ya sanya ta sassauta kukanta
"Mama ki zauna zan fad'amaki komai."
Mama ta zauna jiki sanyaye
"Ina sauraronki,kiyiazamar sanar dani kada jinina ya hau."
Ta dubi mamanta
"Yaya jafar ne yazo."
Mama ta zaro idocike da mamaki
"Jafar dai na kasuwa? Menene ya kawoshi?"
Ta tambaya cike da zargi,Ladi ta daure ta zayyane mata dukkan abunda ke faruwa. Bata kai k'arshe ba taji Mama ta wanke mata fuska da kyakkyawan mariwanda ya sanya Ladi zaro ido rike da fuska tana kallon mahaifiyarta. Tunda ta taso Mama bata tab'a kai hannu kan fuskarta ba,bata tab'a yunkurin marinta ba sai yau.
"Kin bani mamaki Hadiyya! Lamarin nan ya sanyamin tsoronki! Ina maki kallon mai hankali ashe har yanzu kuruciya yana yawo a kanki?! Waye Jafar! Waye shi? Me yake dashi da har yafi sauran maza?!! Akanshi kika sab'awa Ubangijinki! Kikayi k'arya!!!! Ashe zaki iya aikata abu har haka ba tare da sanina ba? Ina tarbiyyar dana kwashi shekaru ina baki? Akan soyayya kinyi fatali da ita?!! Wace riba kika tsinta da hakan? A yanzu ki fadamin me Jafar yayi maki a karshe? Wallahi kin bani kunya! Ba shakka kin zamo mini abun tsoro,matukar auren kikeso dole ne ayi maki tunda har zaki iya wannan aikin akan da'namiji!!!!"
A fusace Mama ta fad'a d'akinta. Nan ta bar Ladi tana rusa ihun kuka,tana mai cike da dana sanin biyewa zuciyarta. Ashe ba'a soyayya ta dole? Bata yiwuwa da k'arya? Tabbas mafi yawan son da za'a dunga karyace karyace babu komai a karshensa sai bakin ciki da bala'o'i.
Gaba d'aya taji ta tsani kanta,ta tsani aikin data aikata. Yanzu meye ribarsa? Wane sakamako ta tsinta a karshe?
"Astagfirullah!"
Ta fad'a a fili sannan ta mike tayi d'akin.
******
Allah ne Ya tserar dashi. TaimakonSa ne ya maidoshi gida lafiya. Dakyar ya iya bud'e d'akinsa ya shiga.
Zubewa yayi a k'asa yana mai sauke ajiyar zuciya akai akai. Zafi yakejin zuciyar tana masa, damuwa da bakin ciki sun tarar masa. Har lokacin bai bar ganin yanda lamarin ya kasance ba a idonsa. Wani sa'in sai ya d'auka ko mafarki yakeyi. Ashe daman Ladi ce Hadiyya?!!! Innalillahi
Ya dafe kansa da hannu biyu ya runtse ido a yayinda yakejin ya tsani abunda ta aikata! Ladi kam ta cuceshi. Kafin kace me,tuni kansa ya soma sarawa. Duk da hakan bai bar cigaba da matsawa kwakwalwarsa da tunani ba. Kalamanta suna yawo a kwakwalwarsa,dayanda suke daukar lokuta mai tsawo suna hirarraki duk zantukan soyayya. Oh Jafar! Har tsawon wane lokaci ya dauka yana soyewa da Ladi mai abinci?.
Toh wai ma ya akayi ta samu lambarsa? Yayi shiru yana tunanin,nan da nan ya tuna ranar da Ladi ta nemi lambar wayarsa.
Ya lumshe ido yana dafe goshinsa
"Ya Salam!"
Ya fad'a a bayyane,wayarsata soma k'ara ko kallonta baiyi ba har ta tsinke aka k'ara kira. Ya duba,ganin Siyama ce ya sanyashi d'agawa dakyar.
"Ina jinki Siyama."
Ta ja tsaki
"Bacci ka soma ma? Lallai Jafar,kana sane cewar yau gaba d'aya bakayi kirana ba bayan kasan na kusa arba'in gashi har yanzu bakayi batun dinkunan da akeyi na yawon arba'in ba."
Damuwa ta k'ara yawaita,ya rufe idanuwansa yana mai cije lebbansa na k'asa kafin ya samu damar furzar da numfashi
"Kina neman ninkamin damuwa akan wacce nake ciki. Please whatsoever ki bari da safe sai muyi maganar yanzu ina fama da ciwon kai. Ya Faruk?"
Maimakon ta amsa sai ta hau magana cikin zafi zafi
"Ba damuwarka bace,da ace ka damu dashi ai da babu abunda zai hanaka kirana da safe. Wallahi Jafar duk wasu take taken ka a kwanakin nan ina lura dasu. Duk ka bi ka chanja,yanzu don Hajiya tace ka bar zuwa laifi tayi ne? Na tabbata yanzu baka damu da...."
Yayi azamar kashe wayarshi gaba d'aya domin hakika bashi da wannan lokacin na sauraron shirme da shiriritar Siyama,abubuwandake gabanshi ma matsala ce babba. A daddafe yayi sallar isha'i sannan ya kwanta. Nan ma zuciyarsa tace bai isa ba,bazai barta da damuwa ba idanuwansa su runtsa,duk sanda zai rufe ido fuskarta yake gani. Ga tsananin ciwon da kanshi yakeyi dole saida ya mik'e ya sha magani.(hmm angayamai so wasane!)inbesaniba yatan bayiAbdool......
Lokacin ko karfe tara batayi ba ma hakanan bashi da karfin da zai k'ara fita daga gida.
****
Acan kuwa yana katsewa Siyama kiran,tayi kwafa ta k'ara bibiyarsa saidai cikin rashin sa'a wayar a kashe. Rumaisa wacce bata sati d'aya bata zo gidan ba,tana daga zauna akan kafet ta dubeta fuska a daure
"Ya kukayi?"
Siyama ta dubeta
"Bansan me Jafar yake nufi ba anti,wai cewa yayi na kyaleshi yaji da damuwarshi. A karshe ma kafin nakai ga karasa magana ya kashe wayar gaba daya."
"Kajimin d'an kaza kaza!!!!,(ta antayo mishi ashariya). Lallai wuyansa ya isa yanka! Hajiya da alama bashi da niyyar bada kud'ad'en nan,gashi dai kowa a dangi zuba ido yake yaga irin kwalliyar da zata ci bayan arba'in. Haba Hajiya,kayan Siyama meye mararbarsu da tsummokarai? Banda kala uku na fitar suna da yayi,banga wasu masu kyawun fita unguwa ba a kayanta duk taci ubansu."
Hajiya dake rike da Faruk ta gama goge mishi kashi da wiper ta chanja mishi famfas ta tab'e baki tana mai nuna Siyama sakarce
"Ai kinga wannan! Wallahi duk abunda ke faruwa ita ta janyowa kanta. Ta biyewa soyayyar banza gashinan tana rayuwar bakin ciki. Don ubanta an gayamata yanzu a wannan zamanin ana yin auren wata soyayya? Soyayyar wofi kawai,ke bari kiji na fadamaki nan da kike ganina ban yarda na auri ubanku ba saida na tabbatar yana da gidan rana. Allah Ya jikan indo(mamanta) bata tab'a runtsawa ba saida ta tabbatar na sameshi don hutu take hangomin. Ai d'an hutu sai gidan hutu. Ban tashi nasan wata wahalar rayuwa ba,family namu gaba d'aya,familin Abba Tukur babu inda ba'asan mu ba a fad'in garin nan saidai bak'o. A zamanin marigayi Abba Tukur mahaifina wane irin tashen arziki ne baiyi ba? Shiyasa bana shiri da marasa hannu da shuni. Ke kam kin yiwa kanki,har kunya nakeji kawayena da yan sa idon gidanmu su zo suga yanda kike jego da yaronki. Kin yiwa kanki Siyama,kin bashi fuska ya rainaki."
Siyama tuni ta soma hawaye,ita kam tana son mijinta batajin dad'i zantukan Hajiya saidai fa akan dinkunan nan za'ayita da Jafar. Domin kuwa dole ne ya bayar da kud'ad'e.
Rumaisa tace
"Yanzu Hajiya dai kiyi mishi magana don Allah."
Hajiya ta mike ta kwantar da yaron a gadonshi
"Shikenan,gobe zan nemeshi."
Daga haka suka shiga hira,duk munanan shawarari suke bawa Siyama akan Jafar. Kiran da Abba ya shiga kwalawa Hajiya ne ya sanyata fita da sauri. Sukayi shiru a tsorace Allah Ya baijisu ba dai.
Fuska a had'e ya dubi Hajiya
"Ina Rumaisa?"
Hajiya ta juya ta kwala mata kira,a d'arare ta fito daga d'akin,yaronta na uku,Mannir yana tare da Abba. Ta durkusa
"Gani."
"Wallahi daga yau kika k'ara zuwa gidan nan a kwanakin nan sai na sab'a maki! Wannan ai sakarcin banza ne,ace ganin mijinki matafiyi ne shikenan daga haihuwa kinyita min zarya a gida? Toh ina mai tabbatar maki zan b'ata maki rai wallahi!! Ki tashi ki ja yaranki ku barmin gida.! Munafuka kawai!! Ina sane da halayyarki,duk rashin kunyar da kike yiwa kishiyar surukarki da ita kanta surukar taki duk yana dawowa kunnena! Bari shi Nuran ya dawo,tunda yana tsoranki ni zanyi maganar!"
A fusace yayi d'akinsa ya barsu anan jugum jugum,da gudu gudu Rumaisa ta had'a kawunan yaranta su biyar ras suka tafi.👬👭
Good morning my b loves frnds...!